Mutanen da basu gaza 9 ne ba suka rasa rayukansu a wani hatsarin mota da ya faru akan babbar hanyar Kano zuwa Zaria a yayin da wasu uku suka jikkata.
Mai magana da yawun hukumar kiyaye afkuwar hatsura ta ƙasa FRSC reshen jihar Kano, Abdullahi Labaran a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba ya ce hatsarin motar ya faru ne a ranar Talata 10 ga watan Satumba a garin Kura dake jihar.
Labaran ya ce hatsarin motar da ya shafi mutane 12 ya rutsa da wani babur É—in Adaidaita da wata babbar mota.
“Abin takaici mutane 9 ne suka rasa rayukansu a hatsarin a yayin da wasu uku suka samu raunuka. An garzaya da mutanen babban asibitin garin Kura domin samun kulawar gaggawa.”
“Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa yinkurin wuce wata mota ba bisa ka’ida ba ne ya kai ga Æ™wacewar motar har ta kai ga hatsarin,” ya ce.
Kwamandan hukumar ta FRSC a jihar Kano, Ahmad Muhammad ya miÆ™a saÆ™on ta’aziyarsa ga iyalan waÉ—anda suka mutu tare da jajantawa mutanen da suka jikkata.