Muna zargin sojoji da kawo hargitsi a zaben Ribas – INEC

Getty Images

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Hukumar zabe a Najeriya INEC ta zargi rundunar sojojin Najeriya da kuma wasu gungun ‘yan ta’adda dauke da makamai da kawo hargitsi a zaben gwamna da na ‘yan majalisar dokoki a jihar Ribas da ke kudancin kasar.

Sanarwar da Kwamishinan hukumar mai kula da watsa labarai da kuma wayar da kan masu zabe Festus Okoye ya sawa hannu ta bayyana cewa hukumar zaben ta dakatar da duk wasu harkokin zabe a jihar Ribas a ranar 10 ga watan Maris saboda yawan hargitsi da aka rinka samu musamman wajen tattara sakamakon zabe wanda a dalilin hakane hukumar ta kafa wani kwamitin bincike domin bin diddikin matsalar da kuma gabatar da rahoto a cikin sa’o’i 48.

Mista Festus ya bayyana cewa hukumar ta tattauna a ranar 15 ga watan Maris bisa rahoton da kwamitin da ta kafa ya gabatar mata inda a yanzu haka hukumar ta gano cewa an gudanar da zabe a akasarin rumfunan zaben jihar kuma an sanar da sakamako.

Sanarwar ta ce ”akwai sakamakon kananan hukumomi 17 cikin 23 a hannun hukumar zabe kuma an bayyana sakamakon mazabu 21 cikin 32 kafin dakatar da al’amuran zabe a jihar; kuma sojoji da wasu ‘yan ta’adda dauke da makamai sun kai samame cibiyoyin tattara sakamakon zabe inda suka razana jam’ian INEC kuma suka kama wasu ba bisa ka’ida ba.”

Mista Okoye ya bayyana rashin jin dadinsa a kan yadda sojoji da wasu ‘yan ta’adda dauke da makamai suka kawo tsaiko a wajen zaben a kokarinsu na sauya abinda mutane suke so kuma suka zaba.

Ya ce hukumar za ta tattauna da manyan jam’ian tsaro a matakin tarayya da kuma kwamitin hukumomin tsaro a matakin jiha domin tabbatar da an karkare abinda ya yi saura na zaben cikin lumana.

Ya kuma ce a ranar Laraba hukumar za ta fitar da cikkakun bayanai a kan yadda za a karasa zaben.

Jihar Ribas na cikin jihohi shida da hukumar INEC ta bayyana cewa zabensu bai kammala ba.

Haka ma jihar Bauchi na daya daga cikin jihohin da hukumar ta bayyana zabenta a matsayin wanda bai kammala ba sai dai a yanzu haka hukumar ta fitar da sanarwa inda ta ce a ranar Talata ne za ta ci gaba da tattara sakamakon zabe na Tafawa Balewa inda daga nan kuma ake sa ran bayyan sakamakon zaben gwamnan na Bauchi.

Jama’a da dama a kasar sun yi korafi bisa yadda hukumar ta bayyana zaben jihohi shida a matsayin zaben da bai kammala ba inda kuma jihohi biyar cikin shida jam’iyyar adawa ta PDP ce a kan gaba.

More News

Mutane uku sun mutu a ruftawar wani ginin bene a Kano

Hukumar Bada Agajin Gaggawa Ta Ƙasa NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane uku bayan da wani bene mai hawa uku ya ruguzo a unguwar...

Ganduje Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Shirya Zanga-Zangar Neman A Sauke Shi

Shugaban jam'iyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin jihar Kano ta jam'iyar NNPP ita ce ke da alhakin shirya zanga-zanga iri...

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...