Muna nan APC amma Atiku zamu zaba – Babachir Lawal

0

Tsohon sakataren gwamnatin tarayya kuma jigo a jam’iyar APC, Babachir David Lawal ya ce suna nan a jam’iyar APC amma kuma Atiku Abubakar za su zaba.

Babachir ya ce jam’iyar APC ba za ta ci zaben shugaban kasa ba saboda yadda ta tsayar da Musulmi da Musulmi a takarar shugaban kasa.

A wata tattaunawa da BBC, Babachir ya ce shi da sauran mutane sun goyi bayan Bola Tinubu ya lashe zaben fidda gwani a jam’iyar APC amma daga baya sai suka gano ya dade yana boye musu aniyarsa ta zaben Musulmi a matsayin mataimaki.

Ya kara da cewa a yanzu baya goyon bayan Tinubu kuma APC ba za ta ci zaben shugaban kasa ba.

Lawal ya ce jam’iyar Labour Party tayi kokarin shawo kan su su mara mata baya amma suka ki amincewa.