Mummunar ambaliyar ruwa ta halaka mutane 3 a Kebbi

An tabbatar da mutuwar mutane uku sakamakon mamakon ruwan sama da aka shafe sa’o’i da dama ana yi a ranar Asabar a unguwar Dakingari da ke karamar hukumar Suru a jihar Kebbi.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Shugaban karamar hukumar Suru, Alhaji Muhammad Lawal Suru, ya ce ambaliyar ta dauki tsawon sa’o’i da dama tare da lalata dukiyoyi na miliyoyin naira.

Ya ce “Bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya, ruwan da ke gangarowa daga tsaunukan da ke kewayen garin Dakingari ya taimaka wajen ambaliyar.

“Sama da shekaru ashirin muna fama da ambaliyar ruwa idan ana ruwan sama duk shekara. Gwamnatocin Nasamu Dakingari da Atiku Bagudu da suka shude sun gina magudanan ruwa a garin domin magance matsalar amma ba su hana ambaliyar ruwa ba duk shekara”.

Ya ba da shawarar cewa za a iya hana ambaliya idan za a iya gina shinge na kankare da hanyar fitar ruwa a kewayen tsaunukan.

Ya yi kira ga al’ummar yankin da su daina gine-gine a magudanan ruwa da kuma zubar da shara.

Ya ce karamar hukumar ta tallafa wa wadanda abin ya shafa da kayayyakin agaji, sannan ta tuntubi gwamnatin jihar da sauran hukumomin da abin ya shafa domin ci gaba da daukar matakan shawo kan lamarin.

More News

Ƴan sanda sun kama mutane 50 kan rikicin da ya faru a wata kasuwa a Lagos

Rundunar ƴan sandan jihar Legas ta kama mutane sama da 50 da ake zargin suna da hannu rikicin da ya faru a kasuwar Ile...

Ƴan Sanda sun kama wanda ya shirya kai harin jirgin ƙasar Abuja-Kaduna a shekarar 2022

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Abdullahi wanda ake zargi da kitsa harin jirgin ƙasar da...

Ƴansanda sun kama wanda ya kitsa harin da aka kai wa jirgin ƙasa a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a ranar Alhamis, ta sanar da kame wanda ake zargin ya shirya harin da aka kai a jirgin ƙasan Abuja-Kaduna...

Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani ɓangare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane...