Motar da Adam Zango ya ce ya saya milyan 23 ba tasa ba ce, tawa ce na ba shi shan miya – Z-Preety

Fitacciyar jarumar finafinan Hausa, Zulaihat Ibrahim, wacce aka fi sani da Zpreety, ta yi wata muhimmiyar magana akan motar da Adam Zango yace ya saya naira miliyan 23.

Zulaihat wacce aka fi sani da Zpreety ta bayyana cewa wannan magana ba haka take ba, inda ta ce mota dai tata ce ta ara masa. Ta kara da cewa ta yi hakan ne domin ta nunawa duniya yadda take girmama Adam Zango, amma kuma sai ya ɓuge da yi wa mutane karya.

Zulaihat ta bayyana cewa motar nan da Adam Zango ya dinga sanyawa a kafafen sada zumunta ba tashi bace motarta ce.

Ta bayyana hakan ne a cikin wani bidiyo da ya dinga yawo a kafafen sada zumunta, inda aka nuno ta a tsaye kusa da motar tana magana.

Zulaihat din ta ce “Mutane na taa tambaya ta cewa dana sami kudin wakar babban yaro mai na yi da shi, gaskiya ce nake so na fada yau, motar nan da kuka gani Baba Adamu yana hawa tsakani da Allah tawa ce.

“Da aka bani ita don nake hawa, sai na ga cewa yana da kyau ka girmama na gaba gare ka, sai na dauka na ba shi akan zai hau na tsawon wata biyar daga nan zan karba na cigaba da amfani da motata.”

A jikin bidiyon Zulaihat ta nuna asalin motar Adam Zango, domin ta kara tabbatarwa da mutane cewa motarta ce.

“Ina dai so na nunawa duniya ta san ainahin abinda ke faruwa ne saboda kowa ya san cewa karya babu kyau.” Makonnin da suka gabata ne dai hotunan jarumi Adam Zango akan wata jar mota suka dinga yawo a shafukan sada zumunta, inda aka bayyana cewa ya sayi motar naira miliyan 23.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miƙata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaƙi da yiwa tattalin arzikin ƙasa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...