Milan da Inter za su gina sabon filin wasa |Sport news

AC Milan Inter Milan

Hakkin mallakar hoto
Reuters

AC Milan da Inter Milan sun bayyana shirin da suke yi na gina sabon filin wasa da zai ci ‘yan kallo 60,000, kuma kusa da filin San Siro.

A cikin tsarin da kungiyoyin biyu ke son gudanarwa har da gyaran filin wasa na San Siro.

Sabon filin wasan da suke son gina wa zai ci fam miliyan 576 da zai kai shekara uku kan a kammala ginin.

Haka kuma kungiyoyin na son tuntubar magoya bayansu kan wannan shirin da suka tsara kafin aiwatar da shi.

Shugaban AC Milan Paolo Scaroni ya ce ”AC Milan da Inter Milan na amfani da San Siro sama da shekara 70”.

Kungiyoyin biyu sun zabi gina sabon filin wasa ne maimakon gyara San Siro wanda za su kashe fam miliyan 452, za kuma su yi hasarar kudin shiga fam miliyan 102 a lokacin gyaran.

Haka kuma gyaran San Siro zai dauki shekara shida kan a kammala, sannan wurin zaman ‘yan kallo ba zai kai wanda sabon fili dai dauka ba.

More News

Kotu Ta Hana PDP Cire Shugaban RiÆ™on Jam’iyar

Wata Babbar Kotun Tarayya dake Abuja ta hana jam'iyar PDP dakatar da Umar Damagum daga matsayinsa na shugaban riƙon jam'iyar. Mai Shari'a  Peter Lifu shi...

Tinubu Ya Dawo Abuja Daga Ziyarar Aiki Da Ya Kai  Saudiya da Nezaland

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya dawo Abuja bayan ziyarar aiki da ya kai ƙasashen Saudiya da Nezaland. A ranar 22 ga watan Afrilu ne...

CBN ya dakatar da kudirinsa na sa bankuna su riƙa cajar kwastomominsu

Babban bankin Najeriya ya umarci bankunan da su dakatar da cajin kudaden ajiya har zuwa ranar 30 ga Satumba, 2024.Babban bankin ya bayyana hakan...

Ƴansanda sun kama likitan bogi

Rundunar ‘yan sanda ta Zone 2, Onikan, Legas, ta kama wani likitan jabu mai shekaru 37, kuma ma’aikacin lafiya, tare da zargin amfani da...