Messi zai buga wa Argentina kwallo ranar Juma’a

Lionel Messi

Hakkin mallakar hoto
Quality Sport Images

Image caption

Har ila yau Argentina za ta kara da Uruguay a birnin Tel Aviv a ranar Litinin

Lionel Messi na cikin tawagar da za ta wakilci kasar Argentina a wasan sada zumunci da za ta fafata da Brazil a kasar Saudiyya ranar Juma’a.

Wannan ne karon farko da dan wasan zai fito a wasa irin wannan tun bayan korarsa daga filin wasa a gasar Copa America a fafatawar kasarsa da Chile cikin watan Yuli.

An dakatar da dan wasan na Barcelona, mai shekara 32, har tsawon watanni uku bayan da ya ayyana cewa ana magudi a gasar.

Hakazalika dan wasan Aston Villa Douglas Luiz a karon farko na cikin tawagar da za ta wakilci Brazil a wasan.

Wannan shi ne karo na farko da kasashen biyu biyu za su yi wasa tun bayan da Brazil ta doke Argentina da ci 2-0 a wasan kusa da na karshe a gasar Copa America.

Brazil ta kasa cin nasara a wasanni hudu tun lokacin, da ta sha kaye a hannun Peru da ci 1-0 a watan Satumba, yayin da Argentina ta samu nasara a wasanni hudu a lokacin da aka dakatar da Messi, inda ta doke Ecuador 6-1 a watan da ya gabata.

Har ila yau Argentina za ta kara da Uruguay a birnin Tel Aviv a ranar Litinin, amma ana ganin za a iya dakatar da wasan saboda rikicin da ke faruwa a Isra’ila.

Ita kuwa Brazil za ta kara da Koriya ta Kudu a birnin Abu Dhabi ranar Talata, wanda zai kasance wasansu na karshe kafin fara wasannin share fagen shiga Gasar Cin Kofin Duniya na 2022 da za fara a watan Maris.

More from this stream

Recomended