Messi ya ci fenareti a Saudiyya

Messi

Hakkin mallakar hoto
Reuters

(BBC Hausa)

Lionel Messi ya ci wa Argentina kwallo daya, da ta bata damar doke abokiyar hamayyarta wato Brazil, a wasan sada zumunta da suka buga a Saudiyya.

Tunda farko mai tsaron raga Alisson ya ture bugun daga kai sai mai tsaron gida da Messi ya buga masa, to amma Messi ya mai da kwallon inda kuma ta shiga raga.

A yanzu Messi ya ci wa Argentina kwallo ta 69 kenan.

Shima dan wasan gaban Brazil Gabriel Jesus ya zubar da bugun daga kai sai mai tsaron gida da Brazil ta samu.

Messi na dawowa ne daga dakatarwar da a ka yi masa ta watanni uku, bayan ya zargi cewa an daurewa Brazil gindi a Copa America, wanda hakan ya sa ta lashe gasar a watan Yuli.

An tsara Argentina za ta fuskanci Uruguay a Tel Aviv ranar Litinin, to amma akwai yiwuwar a soke wasan saboda tashin hankali da ke faruwa a Isra’ila.

To amma Brazil za ta kara da Korea ta Kudua birnin Abu Dhabi ranar Talata, wasan sa da zumunta na karshe kafin fara wasannin share fagen gasar cin kofin duniya ta 2022 da za’a fara watan Maris.

A sauramn wasannin sada zumunta da aka buga Uruguay da doke Hungary 2-1, yayin da Ecuador ta lallasa Trinidad & Tobago 3-0.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...