Menopause: Amsar tambayoyinku kan ko shekarun manyantakar mace na illa ga rayuwar aurenta

Ranar Talata ita ce ranar da aka ware don duba batutuwan da suka shafi shekarun daukewar jinin haila ga mace.

Don haka ne muka sake wallafa muku wannan rahoton da muka taba wallafa shi ranar 17 ga Junairun 2018.

Mata na hawa mataki-mataki a rayuwarsu, kamar tun daga haihuwa da ‘yan matanci har zuwa girmansu da tsufansu.

A ko wanne mataki kuma sukan ci karo da al’amura daban-daban ko dai na sauyin tsarin halitta ko na rayuwa, kamar jinin al’ada da aure da haihuwa da raino.

Wani mataki kuma da ke kawo sauyi sosai a rayuwar mace, shi ne na daukewar jinin al’adarta gaba daya, da kuma tsayawar haihuwa, wanda a turance aka fi sani da Menopause.

Dakta Yelwa, kwararriyar likita a asibitin Maitama da ke Abuja, ta ce Menopause mataki ne na manyantar mace da za ta daina yin al’ada.

Kuma mace na shiga wannan mataki ne idan ta yi tsawon watanni 12 ba tare da ganin jinin al’ada ba.

A yayin da mace take girma tana al’ada, yawan jakar miliyoyin kwayayen da ke jikinta na raguwa har zuwa lokacin da za ta shiga matakin da al’adar za ta dauke baki daya.

Daukewar jinin al’ada da ake kira Monopause a turance ba cuta ba ce, illa lokaci ne da idan shekarun mace sun kai zai same ta.

Mace kan shiga mataki na menopause da karfinta ba sai ta tsufa juguf ba.

“Mace za ta ji ba ta sha’awar namiji saboda raguwar wasu sinadarai da suke taimakawa jini da ake kira Oestrogen” a cewar likita.

Akwai alomomi da dama da mace za ta fuskanta a lokacin da ta shiga mataki na Menopause.

Mace za ta iya daina ganin al’ada idan ta kai shekara 45 zuwa 55, wato shekarun da mata ke fuskantar daukewar al’ada ke nan.

Amma likita ta ce mafi yawanci wasu tun daga shekara 51 suke daina ganin al’ada.

“Mace kan iya fuskantar daukewar al’ada, kafin lokacinta idan misali an yi mata tiyata a wajen haihuwa ko kuma wata matsala ta sa an cire mahaifa.”

Dakta Yalwa ta kuma ce duk wadannan matsaloli ne da kan iya faruwa ga mace a ko wane lokaci.

‘Mace na iya fuskantar daukewar al’ada saboda wadannan matsalolin, ba wai don shekarunta sun kai ba”.

Sai dai kuma likitar ta ce wasu matan kan zarce har shekaru 60 suna jinin al’ada, amma mafi yawanci tsakanin 45 zuwa 55 ne al’ada ke daukewa.

Daukewar al’ada kan zo ne mataki mataki, wato ba lokaci daya ba.

Likita ta ce mace na iya ganin wasu sabbin sauye-sauye da alamu na daukewar al’ada a tsakanin shekara 8 zuwa 4.

‘Sauyin ya shafi sauyin kwanakin al’ada, misali idan mace ta saba yin al’ada duk bayan kwanaki 30 ko 28 to za ta iya ganin kwanakin sun haura zuwa 40, wata ma har wata biyu kafin jinin ya dawo’.

Sannan mace za ta iya ganin sauyi a yawan zubar jinin da ta saba gani.

Likita ta ce idan mace ta saba yin kwanaki biyar ko bakwai, to za ta ga ta dawo tana yin kwanaki biyu, wani lokacin ma kwanakin su karu fiye da bakwai.

Wasu alamomin kuma ga matan da suka shiga shekarun daukewar al’adar, sun hada da gumi, mace za ta ji tana yawan zufa, wanda ba ta saba ji ba, ko da kuwa ba lokacin yanayin zafi ba ne.

Rashin bacci ma wata alama ce, inda mace za ta dade kafin bacci ya dauke ta da dare, ko idan ta farka daga bacci zai yi wahala ta sake komawa baccin.

Haka kuma matan da suka shiga shekarun daukewar al’ada sukan fuskanci matsalar yawan ciwon kai da ciwon gabobi, da kuma mace ta ji ta shiga wani yanayi na bacin-rai.

Sauran alamomin daukewar al’adar ga mata sun hada da sauye-sauye a jikinsu musamman yawan fitsari da zubewar gashi da bushewar fata da farji inda mace za ta ji ba ta son saduwa da mijinta.

“Idan har ta kai wannan mataki, za ta fara jin zafi a lokacin saduwa da miji maimakon jin dadi”.

Likitar ta ce mata za su ga sauyi sabanin kuriciya, ko kuma lokacin da suke ganiyar haihuwa, kamar gushewar ni’ima”, a cewar Dakta Yelwa.

Ta kara da cewa duk wadannan alamomin suna faruwa ne a yayin da sinadarin jini da ake kira ‘oestrogen’ a jikin mace ke yin kasa sosai.

‘Sinadarin shi ke tallafawa al’ada, kuma a yayin da ya yi kasa sosai, yana rage kwari da ingancin kashin mace.’

Ko jini zai dawo bayan shekarun daukewar al’ada?

Likita ta ce bayan daukewar jini a lokacin da Mace ta shiga mataki na menopause, tana kuma iya ganin jini daga baya, kila bayan kamar tsawon wata 10 ko shekara daya.

‘Wani lokaci kuma mace na iya ganin jini bayan ta sadu da maigida a mataki na ‘menopause”.

Amma likita ta ce yana da kyau mace ta tafi asibiti domin a binciki dalilin dawowar jinin.

Me ya kamata mace ta yi kafin Menopause?

Likita ta ce mataki na farko shi ne, ya kamata mace ta fahimci yanayin jikinta, wato ta banbance matsala da kuma matakin daukewar al’ada.

Ya dace mace ta san matsalolin da za ta iya fuskanta a lokacin da ta shiga shekarun daukewar al’ada, kamar sabbin sauye-sauye a jikinta.

Likita ta ce zuwa asibiti zai taimaka a banbance, tsakanin cuta da alamomin daukewar al’ada, domin akwai cututtuka da ke haifar da yawan zubar jini da gudajin jini wadanda ba su da alaka da lokaci na ‘menopause’.

‘Idan jinin yakan zo da yawa har da gudaji, to akwai matsala, ya kamata a tafi asibiti a bincika.’

Haka kuma, idan ana fama da yawan fitsari, a lokacin da mace ta shiga shekarun ‘menopause’ to yana da kyau a tafi asibiti a bincika ko kila cutar ciwon shuga ce ta ci karo da lokacin daukewar al’adar.

Menopause kafin lokacinsa

Wasu mata kan yi koken cewa suna fama da matsaloli da suka shafi alamomi na daukewar al’ada tun kafin su haura shekaru 30.

Matsalolin sun hada da bushewar farji da gushewar ni’ima, lamarin da ke haifar da matsaloli na auratayya tsakanin matan da mazajensu.

Kuma kamar yadda bayani ya gabata, mace kan shiga yanayin ‘menopause’ ne tsakanin shekaru 45 zuwa 55.

Dakta Yelwa ta ce hakan ba ya da nasaba da daukewar al’ada, illa abin da ya kamata matan su yi shi ne su tafi asibiti a yi bincike domin gano matsalolin da ke damunsu.

Ko mace na iya shan wasu magunguna don rage yanayin Menopause?

Ta la’akari da alamomin lokacin manyantakar mace, kamar gushewar sha’awa da rashin sinadarin ‘Estrogen’ da zai haifar da bushewar farji da fata da raguwar ni’ima da kuma raguwar gashin kai, Dakta Yelwa ta ce akwai magungunan da mace za ta iya amfani da su.

Amma kuma ta ce likita ne zai iya diba yanayin mace sannan ya bada shawarwari da kuma magungunan da suka dace.

Likitar ta ce a kasashen Turai wasu matan kan yi amfani da “hormone therapy” wasu nau’in magunguna ko dashen wasu abubuwa domin gyara jiki da farfado da sha’awa da sauran alomin da suka gushe.

“A shagon sayar da magunguna ana sayar da wasu abubuwa da mace za ta iya gogawa a farjinta wanda wurin zai sa ya yi laushi maimakon bushewa”.

Sai dai Dakta Yelwa ta ba mata shawara kafin shan wani magani ya kamata su ziyarci likita domin ya tantance magungunan da suka fi dacewa da za su taimakawa a lokacin manyantakarsu.

Da aka tambayi Dakta Yelwa ko akwai wani tasiri da magungunan gargajiya da ake kira kayan mata za su yi idan mace ta shiga shekarun manyantaka, sai likitar ta ce magungunan na iya haifar da matsaloli ga lafiyar mace.

More News

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miĆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaĆ™i da yiwa tattalin arzikin Ć™asa ne ya hana shi bayyana...