Mece ce makomar yara almajirai a Kano? | BBC Hausa

Kano na daga cikin jihohin da ke da yawan yara almajirai a Najeriya

Yawon bara da sunan almajiranci tsakanin yara kanana na daya daga cikin matsalolin da suka gagari jihohin arewacin Najeriya a tsawon shekaru.

Ko a baya-bayan nan an ga yadda gwamnatocin jihohi ke kokarin daukar matakin dakile wannan dabi’a.

A jihar Kano, gwamnati ta fara kame yara almajirai da ke gararamba a kan tituna tana mayar da su jihohinsu ko kuma gaban iyayensu.

A tattaunawarta da BBC, kwamishinar mata ta jihar Kano Zahra’u Muhammad ta ce ya kamata malamai su gane cewa tsarin almajirci abu ne da ya tsufa, bai dace a ci gaba da shi ba.

Tun kafin wannan lokaci, Kano din ce ce ta fara mayar da dalibai jihohinsu na asali bayan bullar cutar korona, inda daga baya wasu jihohin suka bi sahu.

A tsawon shekaru yawon almajiranci tsakanin yara kanana na daya daga cikin matsalolin da suka gagari jihohin arewacin Najeriya.

Gwamnatoci dai sun damu da wannan matsala ce saboda irin hadurran da yara kanana kan shiga sanadiyyar almajiranci da kuma rashin samun ilimin zamani.

Hadurran da yara almajirai ke fadawa

  • Rashin abinci
  • Saurin kamuwa da cututtuka
  • Fuskantar danniya da take hakki
  • Rashin samun ilimin zamani

In ji Dr. Aliyu Tilde, kwamishinan ilimi na jihar Bauchi.

Makarantun tsangaya na gwamnati

BBC ta kai ziyara a daya daga cikin makarantun da gwamnatin tarayya ta gina a Jalawa, da ke karamar hukumar Warawa cikin jihar Kano, sai dai makarantar ba ta a cikin yanayi mai kyawu.

Makaranta ce mai yawan dalibai 510. Matsalolin da ke addabar makarantar sun hada da:

  • Rashin kujeru
  • Rashin wutar lantarki
  • Lalacewar gine-gine
  • Rashin tsaftar muhalli
  • Rashin isassun gadajen kwanciya
  • Rashin tsari mai kyau na kula da lafiyar dalibai

Shugaban makarantar Mallam Isma’il Tafida ya ce “Mukan ba marasa lafiya farasitamol ne ko filajin, amma idan abin ya fi karfin haka muna mayar da su ne wurin iyayensu.”

Me gwamnati ke yi a kai?

A lokacin da BBC ta tuntubi kwamishinan ilimi na jihar Kano Muhammad Sanusi Kiru game da rashin kyawun yanayi na makarantar ya ce ba ya da rahoton hakan amma kuma bai yi mamaki jin hakan ba.

Sai dai a cewarsa a hakan ma an yi wa almajiran gata ne “Alamajiri da ba ya da wurin kwana, alamajiri da yake kwana a tashar mota, alamjiri da yake cin abinci a karkashin kwalbati, yanzu kuwa an dauke shi aka daraja ji aka kai shi makaranta, yana kwance fanka na fifita shi? Ba za a hada yanayin da suke a baya da yanda suke a yanzu ba.”

Ya tabbatar wa BBC cewa gwamnati za ta duba lamarin.

Shigar da karatun boko a makarantun allo

Wani tsarin da gwamnatin jihar ta bullo da shi shi ne na cusa karatun boko a makarantun allo da ake da su.

A karkashin wannan shiri gwamnati za ta tura malaman boko su rinka koyar da almajirai darussa irin su turanci da lissafi a ranakun Alhamis da Juma’a na kowane mako, wato ranakun da ba a karatun Kur’ani.

Haka nan kuma gwamnatin ta ce za rinka tallafa wa alaranmomin da kayan abinci da kuma albashi a duk wata.

BBC ta ziyarci makarantar Mallam Ayuba mai almajirai da ke Gogel, malamin ya ce a tunaninsa tsarin ba zai ci nasara ba saboda a al’ada Alhamis da Juma’a ranaku ne da aka ware na hutu da kuma neman taro da sisi ga almajirai, saboda haka bai kamata a ce za a takura wa almajiran ba.

Ya ce sau da da dama ko da malaman da ke koyar da darussan ilimin zamanin sun zo ba su samun daliban, domin kuwa sukan fita zuwa wurin sana’a ko kuma neman kudin da za su sayi sabulun wanki.

Ya kuma tabbatar wa BBC cewa baya ga malaman da ake turowa babu wani abu da suka gani da sunan tallafi. Ba a turo masu tallafin abinci ko kuma kudin da aka yi alkawari ba.

A nasa ra’ayin ba ya tunanin tsarin zai yi nasara.

Sai dai shugaban hukumar ilimin bai-daya ta jihar Kano Dr. Danlami Hayyo, ya ce sanya karatun boko a tsarin makarantar allo abu ne da ake bi daki-daki.

A cewarsa za a rinka biyan alaranmomi kudi duk wata a matsayin albashi sannan kuma za a dauki matan alaranmomin aiki domin su rinka dafa abinci ga almajirai.

Mafita

A cewar Dr. Aliyu Tilde hanyar da za a iya magance matsalar barace-barace tsakanin kananan yara ita ce a daina tura yara nesa domin neman karatun alkur’ani.

Ya ce kamata ya yi iyaye su rinka tura yaransu makaranta da ke kusa da gida, ta yadda yaran za su samu damar zuwa makarantar boko da na allo, sannan kuma su kasance kusa da iyayensu wadanda za su ba su tarbiyyar da ta dace.

Wannan rahoto ne na musamman da BBC Hausa ke kawo ma ku tare da tallafin gidauniyar MacArthur.

More News

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miĆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaĆ™i da yiwa tattalin arzikin Ć™asa ne ya hana shi bayyana...