Me ya sa Buhari ya ki cire hafsoshin tsaron Najeriya?

[ad_1]

Shugaba Buhari


Masana harkokin tsaro na ganin ci gaba da kasancewar hafsoshin tsaro a kan mukamansu na ta’azzara hare-hare.

Kaimin da wasu ‘yan Najeriya suka yi wajen yin kira ga shugaban kasar Muhammadu Buhari ya sauke manyan hafsoshin tsaron kasar wata alama ce da ke nuna yadda al’amuran tsaro ke kara rikicewa a baya-bayan nan.

Manyan muryoyin da suka koka kan tabarbarewar tsaro a Najeriya a baya-bayan nan sun hada da shugaban majalisar dattawan kasar, Sanata Ahmed Lawan.

Lokacin da majalisar dattawan Najeriya ta koma bakin aiki bayan hutun da ta yi, Ahmed Lawan, wanda shi ne mutum na uku mafi karfin mukami a Najeriya, ya nuna matukar takaicinsa kan hare-haren da mayakan Boko Haram da masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa ke kai wa.

Lamarin ya kazanta a watan jiya inda rahotanni ke cewa ‘yan kungiyar ta Boko Haram sun kashe mutane da dama sannan suka hana tafiye-tafiye kan wasu hanyoyi da ke yankin arewa maso gabashin kasar, musamman hanyar Damaturu zuwa Maiduguri.

Baya ga haka, masu garkuwa da mutane sun ci gaba da cin karensu babu babbaka musamman a jihohin arewa maso yammacin kasar, irinsu jihar Katsina da Zamfara.

Hakan ya sa ‘yan kasar da dama sun nuna matukar kaduwarsu game da wadannan hare-hare ganin cewa gwamnatin kasar ta dade tana yi musu dadin bakin cewa ta murkushe mayakan na Boko Haram, inda take cewa hare-haren da ake kai wa a yankin Najeriya arewa maso gabas na gyauron ‘yan ta’adda ne.

Amma duk da haka ‘yan kasar ba su gamsu ba, inda suke yin kira da a sauya hafsoshin tsaron kasar.

Sai dai da alama babban abin da ya fi tayar da kura game da wadannan kiraye-kiraye shi ne kiran da shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Eyinnaya Abaribe ya yi ga Shugaba Buhari da ya ajiye mulki, yana mai cewa shugaban ya gaza.

Da yake bayar da gudunmawa a zauren majalisar, Sanata Abaribe ya ce “‘Yan Najeriya ba su zabi Babban Sufeton ‘yan sanda ba, ba su zabi shugaban ma’aikatan shugaban kasa ba, ba mu zabi dukkan hafsoshin tsaro ba, ko kuma mai ba da shawara kan sha’anin tsaro.

“‘Yan Najeriya gwamnatin jam’iyyar APC suka zaba a 2015 sannan suka sake zabar ta a 2019. Mun zabe ta ne saboda ta ce za ta iya magance matsalolin tsaro. Tun da kuwa ta gaza ya kamata ta sauka daga mulki.”

Sai dai wannan kira da Sanata Abaribe ya yi ya janyo masa kakkausar suka daga fadar shugaban kasar.

Mai magana da yawun Shugaba Buhari, Malam Garba Shehu, ya shaida wa BBC cewa shugaban kasar ba zai cire hafsoshin tsaron ba saboda kasar tana tsaka da yaki ne.

A cewarsa, “Duk masu kushe ko suka kan manyan jami’an tsaron nan ba sa la’akari da cewa ko an ki ko an so Najeriya a cikin halin yaki take a yanzu.

“A matsayin Shugaba Buhari na tsohon janar a soja, yana sane da lokacin da ya kamata ya yi canjin kwamandoji da kuma lokacin da bai kamata ba.”

Sannan mai magana da yawun shugaban kasar ya ce, Najeriya ta samu kanta a wannan hali ne tun bayan fantsamar kungiyar IS wadda ta faro daga Iraki da Syria, da kuma rikicin Libiya.

“Amma abin lura shi ne kowa ya san cewa Shugaba Buhari na bakin kokarinsa don kare rayuwa da dukiyar ‘yan kasar nan tamu.”

Amma da alama wadannan kalamai ba su gansar da ‘yan Najeriya da ma masana harkokin tsaro ba inda wasu ke ganin hafsoshin tsaron, wadanda tun tuni wa’adinsu na yin ritaya ya wuce, ba za su iya tabbatar da tsaro ba.

Su wane ne hafsoshin tsaron Najeriya?

Manyan hafsoshin tsaron su ne:

  • Manjo Janar Abayomi Gabriel Olonishakin – Babban hafsan hafsoshi.
  • Manjo Janar Tukur Yusuf Buratai – Babban hafsan sojin kasa
  • Rear Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas – Babban hafson sojin ruwa
  • Air Vice Marshal Sadiq Abubakar – Babban hafson sojin sama.
  • Air Vice Marshal Monday Riku Morgan – Shugaban rundunar tara bayanan sirri
  • Manjo Janar Babagana Monguno mai murabas – Mai bayar da shawara kan tsaro.

A watan Yulin shekarar 2015 ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fara nada manyan hafsoshin tsaron kasar guda hudu na tsawon shekara hudu bayan shugaban ya sauke magabatansu.

A shekarar 2019 shugaba Buhari ya tsawaita wa’adin hafsoshin tsaron da wata shida wanda ya kare a watan Disambar shekarar.

Wani mai sharhi kan al’amuran tsaro a Najeriya, Kabiru Adamu ya ce a bisa tsarin dokar kasar, shugaban kasa ne ya ke da ikon nadi ko sauke manyan hafsoshin tsaron.

A cewarsa, “zai iya barinsu su yi shekara biyu sannan kuma bayan shekara biyun, yana da dama ya tsawaita shekarun ko ya sauya su, kuma ga dukkan alama ya zabi ya bar su.”

Ya ce akwai dokokin da suke tafiyar da ma’aikata a fannin sojoji kuma “sun sa hannu a kai kuma a kan haka suke gudanar da aikinsu.”

A ganinsa, masanin ya ce dokokin ba su kai kundin tsarin mulkin kasa ba don haka “a takaice zabi ne ga shi shugaban kasa ko ya nada su ko ya barsu.”

Ya ce tabarbarewar tsaro a Najeriya bai ta’allaka kan manyan hafsoshin tsaron saboda “akwai bangarori 23 wadanda kowanne daga cikinsu yana bayar da gudummawa a wurin harkar tsaro.”

Kabiru Adamu ya kara da cewa “matsalolin tsaro da ake samu matsaloli ne na cikin gida wanda kuma ba matsala ba ce ta soja, matsala ce ta ‘yan sanda da sauran bangarori na tsaron cikin gida.”

“Bai da ce a ware kashi biyar daga cikin kashi 23 a ce su ne da laifi saboda tarihi da ake da shi na mulkin soja akwai fahimtar da yawanci suke da ita cewa duk matsalar soja ne ke haifar da ita.” in ji sa.

“Ita kanta gwamnatin ta Shugaba Buhari ba ta taimakawa wannan fahimtar ba saboda yawanci wadanda ya nada a matsayin shugabannin tsaro kusan yawanci sun rike mulkin soja na da ko har yanzu ma suna rike da shi.” a cewar masanin.

Ya kuma ce amincewar da Buhari ya nuna na kin sauke hafsoshin tsaron ya kara “jaddadawa ‘yan Najeriya cewa wannan laifi na soja ne.”

Masanin ya bayyana cewa “matsalar tsaro da ake fuskanta a Najeriya laifi ne na taswirar tsaron kasar da kuma tsarin da aka yi wa bangarorin tsaro 23.”

Ya kuma dora laifin tsaron da ake fama da shi a kan “rashin hadin kai tsakanin bangarorin tsaron da rashin sa ido da hukuntarwa shi ya kawo halin da ake ciki a kasar.”

“A baya an samu lokuta da wadannan bangarori na tsaro sun yi abin da ya akamata a ce an ladabtar dasu amma ba a ladabtar da su ba.” kamar yadda masanin ya fada.

“Yadda suke gudanar da ayyukansu da yadda suke tafiyar da harkarsu ta kudade, babu sa ido babu waiwaya a kai”

“Shi yasa mai yiwuwa Buhari ya fahimci cewa ba matsala bace ta soji kawai matsaloli ne da yawa.” in ji Kabiru Adamu.

Amma ya ce akwai alamu Shugaba Buhari yana kokarin samar da gyara tun da “a sabuwar taswirar da gwamnatinsa ta fitar a karshen shekarar data gabata, akwai muhimmin canji da aka yi kan yadda ake gudanar da lamuran tsaro.”

“An dauke shi daga kasa an mayar da shi zuwa ga ‘yan kasa,” wanda a cewarsa ‘yan kasa ne suke da muradin yadda suke son a gudanar da harkokin tsaro.

Sai dai ya ce “abin da ya rage shi ne a aiwatar da sabuwar taswirar.”

More News

Mutane uku sun mutu a ruftawar wani ginin bene a Kano

Hukumar Bada Agajin Gaggawa Ta Ƙasa NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane uku bayan da wani bene mai hawa uku ya ruguzo a unguwar...

Ganduje Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Shirya Zanga-Zangar Neman A Sauke Shi

Shugaban jam'iyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin jihar Kano ta jam'iyar NNPP ita ce ke da alhakin shirya zanga-zanga iri...

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...