Me ya hana zanga-zangar #RevolutionNow tasiri a Arewa?

Filin Unity Fountain kenan a Abuja
Image caption

Dandalin Unity Fountain ke nan a Abuja a ranar Lititnin, inda nan ne aka shirya gudanar da zanga-zangar

Zangar-zangar neman “juyin juya-hali” da aka gudanar a Najeriya wadda aka yi wa lakabi da #RevolutionNow ba ta yi tasiri ba ko kadan a arewacin Najeriya, inda ba mu ga kwali mai dauke da rubutu ba daga Kano ko Kaduna ko jihar Neja.

Hatta a Abuja ma da ake tunanin abin zai ja hankali abin ba haka ya faru ba, domin kuwa ‘yan sanda ne da motocinsu kawai a dandalin Unity Fountain lokacin da wakilinmu Ibrahim Isa ya ziyarci wurin.

Sai dai a kudancin kasar abin ya sha bamban, inda a jihar Legas masu zanga-zangar suka fito fiye da ko’ina a fadin kasar.

‘Yan sanda sun rika harba hayaki mai sa hawaye kan masu zanga-zangar tare da kama su da kuma bincika wayoyinsu na salula.

Jim kadan kuma bayan kura ta lafa ne aka ga ‘yan sandan suna murnar korar masu zanga-zangar.

Me yasa ba ta yi tasiri ba a Arewa?

“Ai ba a ma san da kiran da a fito zanga-zangar ba a arewa, idan ba mutanen da suke kan shafukan sada zumunta ba. Ba a san da ita ba har sai bayan da aka kama Sowore,” in ji Malam Kabiru Sufi na kwalejin CAS Kano.

Omoyele Sowore shi ne dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar AAC a zaben watan Fabrairun 2019 da aka yi a Najeriya, kuma shi ne jagoran gangamin “Take it Back” wadanda su ne suka shirya zanga-zangar ta #RevolutionNow.


Omoyele Sowore shi ne mawallafin jaridar Sahara Reporters

A ranar Asabar ne kuma jami’an tsaro na farin kaya wato DSS suka kama Sowore bisa zargin “yunkurin tayar da tarzoma” a Najeriya.

Kabiru Sufi ya kara da cewa hatta wadanda suka san da kiran ma akwai wadanda ba su yarda da manufarta ba, domin kuwa sai bayan ya yi takara ya fadi sannan ya ce a fito zanga-zanga.

“Suna cewa wanda ya saba bin hanyar lumana mai ya sa kuma yanzu zai bi wata hanya daban”, in ji shi.

Wakilin BBC a Kano Mansur Abubakar ya ce jama’a a birnin sun yi ta yin harkokinsu na yau da kullum kuma babu wata alamar zanga-zanga a birnin a ranar Litinin.

Kazalika, rahotanni sun nuna cewa a jihar Kaduna kuma shari’ar jagoran mabiya Shi’a ce ta dauke hankalin mafi yawan jama’a a birnin.

“Karin abin da ya jawo rashin nasararta a arewacin Najeriya shi ne cewa, ba a fadi inda za a gudanar da ita ba a jihohin arewa sabanin na kudu da kuma Abuja.”


A ranar Lititnin din ne dai kotu ta zauna kan neman belin Zakzaky a birnin Kaduna
. Babu mamaki rashin ‘yan arewa a cikin masu shirya zanga-zangar ya taka rawa sosai, kuma Kabiru Sufi ya ce har ma a shafin Sowore na Facebook ba a ganin ‘yan arewan sosai.

“Ko a zauren Facebook da Sowore ya bude za ka ga babu ‘yan arewa sosai. Da yawa za ka ga saka su kawai aka yi a ciki kuma wasu da dama sun fita daga baya.

Ganin cewa an shirya zanga-zanga ta kasa baki daya a baya wadanda kuma suka yi tasiri har a jihohin arewar, Sufi ya ce bambancinsu shi ne akwai tasiri na kungiyoyin da suke shirya irin wadannan tarukan.

“Yawancin zanga-zangar da aka yi a baya na kungiyar kwadago ne wadda kuma take da tsari. Kamar zanga-zangar cire tallafin mai da aka yi, ai an fadi inda za a yi ta a jihohin arewa da kuma yadda za a yi ta.

“Da a ce an samu tsari din da ba za a rasa wadanda za su shiga ba, kuma idan aka fara wasu za su yi sha’awa su ma su shiga.”

Wasu na ganin rashin tasirinta a arewa ba zai rasa nasaba da farin jinin Shugaba Muhammadu Buhari ba da kuma ganin cewa jama’ar yankin ba su dade da yi wa shugaban ruwan kuri’u ba a zaben watan Fabrairu.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...