Me Shugaba Buhari zai je yi Jihar Imo, cibiyar kungiyar IPOB?

Shugaba Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya zai kai ziyara zuwa Jihar Imo da ke kudu maso gabashin ƙasar a ranar Alhamis, ɗaya daga cikin jihohin da masu fafutukar kafa Biafra ke neman ɓallewa.

Rahotanni daga jihar Imo na cewa Ć™ungiyar ta ba da umarnin jama’a su zauna a gida a ranar Alhamis din saÉ“anin Litinin, wani abu da ake ganin yana da nasaba da ziyarar ta Shugaba Buhari.

Wannan ziyara ita ce ta farko da shugaban zai yi tun bayan da ‘yan kungiyar Ipob suka zafafa kai hare-hare a kwanakin baya kan jami’an tsaro da gine-ginen gwamnati, a fafautukar da suke yi ta ballewa daga kasar.

A baya-bayan nan kungiyar ta umarci al’ummar yankin kudu maso gabashin Najeriya da su dinga zama a gida duk ranar Litinin don nuna turjiya ga mahukunta da kuma jawo hankalin gwamnati ta saki jagoransu Nnamdi Kanu.

Amma saboda wannan ziyara da shugaban zai yi, sai Ipob ta umarci al’ummar yankin da cewa kar wanda ya fita, don nuna wa shugaban karfin ikon da kungiyar ke da shi a yankin.

Sai dai gwamnatin jihar Imo din ta gargadin yan kungiyar ipon da su janye jiki yayin ziyarar, kmaar yadda kwamishinan yada labaran jihar ya fitar a ranar Laraba.

Sannan gwamnati ta yi wa ‘yan jihar umarni su yi watsi da batun Ipob, tare da cewa ta shirya tsaf don tarbar shugaban kasa, kuma jama’a suna dokin tarbar shugaban kasar.

Wadanne ayyuka Shugaba Buhari zai kaddamar?

Shugaba Muhammadu Buhari zai kaddamar da wasu manyan ayyukan da Gwamna Hope Uzodimma ya yi, a cewar mai magana da yawun gwamnan.

Babban jami’in yada labarai na gwamnan Oguwike Nwachukwu, ya ce ziyarar za kuma ta nuna cewa gwamnatin tarayya na son ci gaban jihar Imo.

A cewar Nwachuckwu, ayyukan da Shugaba Buhari zai kaddamar sun hada da:

  • Manyan magudanan ruwa na karkashin kasa na zamani – Chukwuka Nwoha
  • Titin Naze/ Nekede/Ihiagwa
  • Titin Egbeada By-Pass – Amakohia
  • Sabon gini na majalisar zartarwa da ke cikin iidan gwamnatin jihar wato Douglas House.

Wadanne matakan tsaro aka dauka a jihar?

Wani mazaunin birnin ya shaida wa BBC Huasa cewa an jibge jami’an tsaro a fadin birnin ta ko ina. Sannan an kawata garin ta duk inda Shugaba Buharin zai bi.

“Yanayin gari lafiya lau, mafi yawan mutane na murna da zuwan nasa, sannan akwai alamar mutane za su fito su yi harkokinsu, duk da dai akwai wasu masu cike da tsoro.

“Ta ko ina jami’an tsaro ne birjik daga kan sojoji da ‘yan sanda da jami’an farin kaya da kuma na civil defence,” in ji mutumin.

Wani daban kuma ya ce “duk da cewa jami’an tsaron na cikin shirin ko-ta-kwana, to da yawan al’umma kuma na cewa ba za su fita ba. Suna cewa me zai zo ya yi, kuma me zai kawo shi?

“Wasu kuma na ganin ai idan ma ba su fito ba tamkar sun karrama shugaban ne, amma dai masu sana’o’in hannu da dama na ganin gara su fito domin dama rashin fitar ta ranar Litinin ma na damunsu balle kuma a hada da Alhamis,” kamar yadda ya kara da cewa.

A hare-haren da kungiyar Ipob ta zafafa kai wa na baya-bayan ann har da wanda ta kai gidan yari, inda fursunonin fiye da 1,500 suka kubuta, sannan suka cinna wa motoci da gine-gine wuta a birnin Owerri, amma a ‘yan kwanakin nan abubuwa sun lafa, sakamakon matakin da gwamnati ta dauka na dankwafar da kungiyar.

Duk da yake jihar Imo na daga cikin wadanda ke fama da ayyukan ‘yan Ipob, ana ganin wannan ziyara ta kaddamar da ayyuka da Shugaba Buhari zai yi za ta kara wa jami’an tsaro da masu kin jinin raba kasar kwarin gwiwa.

Kana hakan zai kara wa gwamnati kwarjini da jaddada cewa ita ke da cikakken iko a yankin da kuma fadin kasar.

More News

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miĆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaĆ™i da yiwa tattalin arzikin Ć™asa ne ya hana shi bayyana...