Me jama’a ke cewa game da kalaman Dangote – daga BBC Hausa

Aliko Dangote

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Jama’a da yawa na ci gaba da bayyana ra’ayoiyinsu biyo bayan wasu kalamai da attajirin da ya fi kowa arziki a nahiyar Afirka Aliko Dangote ya yi.

A wata hirarsa da ya yi da Gidauniyar Mo Ibrahim, Dangote ya bayyana cewa ya taba zuwa banki inda ya karbo dala miliyan 10 domin ya tabbatar da cewa da gaske yana da kudi.

Dangote ya bayyana cewa da ya je bankin, ya rubuta takardar karbar kudi sai ya karbi kudin lakadan sa’annan ya zuba su a bayan motarsa.

Amma ya bayyana cewa washe gari ya mayar da kudin zuwa banki domin ci gaba da ajiyarsu.

Tun bayan wannan hira, jama’a da dama na ta bayyana ra’ayoyinsu kan wannan gajeran labarin da mai kudin ya bayar.

Wannan na bayyana cewa ”gani ya kori ji, wata kila Dangote a da bai yarda yana da irin wadannan kudin ba.”

Wannan kuma na cewa ”me ya sa bai mallaki kulob din Arsenal ba? Wannan ne lokacin da ya kamata ya yi cinikin kulob din.”

Sai kuma wannan ya ce ”wayyo Allah, ku taimaka ku fada masa cewa kashi daya na kudin nan za su iya sauya rayuwata gaba daya.”

Aliko Dangote wanda dan asalin Kano ne shi ne dan wanda ya fi ko wane bakin mutum kudi a duniya kuma babban mai kudin Afirka kamar yadda mujallar Forbes ta bayyana.

A kwanakin baya ne dai jaridar ta bayyana cewa arzikinsa ya yi kasa a jerin masu kudin duniya, amma duk da haka ta ce Dangote ne a farko a jerin masu kudin Afirka da dala biliyan 10.3.

Sai dai mujallar Forbes din ta nuna cewa matsalar kasuwa ce da kamfanin siminti na Dangote ya fuskanta ya jawo raguwar arzikinsa.

More News

Mutane uku sun mutu a ruftawar wani ginin bene a Kano

Hukumar Bada Agajin Gaggawa Ta Ƙasa NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane uku bayan da wani bene mai hawa uku ya ruguzo a unguwar...

Ganduje Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Shirya Zanga-Zangar Neman A Sauke Shi

Shugaban jam'iyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin jihar Kano ta jam'iyar NNPP ita ce ke da alhakin shirya zanga-zanga iri...

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...