MDD ta roki Tanzania ta daina korar ‘yan gudun hijira

Dubban mutane ne hare-haren masu ikirarin jihadi suka tilasta rabawa da muhallansu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
Dubban mutane ne hare-haren masu ikirarin jihadi suka tilasta rabawa da muhallansu

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga Tanzania da ta daina tilasta mayar da ‘yan gudun hijirar da ke tsere wa tashin hankalin masu ikirarin jihadi a lardin Cabo Delgado na arewacin Mozambique.

Tsawon shekara hudu ana fama da wannan rikici, inda mayakan ke kai hare-hare, suna yawan hallaka jama’a ta hanyar fille kai da kona kauyuka.

Hukumar kula da ‘yan gudun hijra ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce kusan mutane dubu goma ne da suka tsere wa hare-haren masu ikirarrin jihadi daga Mozambique, Tanzania ta tilasta wa komawa inda suka fito.

Daga cikinsu wadanda suka yi kokarin tsallaka wani kogi da ke kan iyakar kasashen, an tare su. Sun kasance ba ta yi, inda suke kwana a filin Allah-Ta’ala cikin sanyi ba barguna.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ‘yan kadan daga cikin ‘yan gudun hijirar da suka iya togewa a kasar ta Tanzania ba su samu wani abinci ko magani ko wata mafaka ba.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
Maharan suna kona kauyuka a arewacin Mozambique

Haka kuma hukumar ta ce akwai matsaloli da suka hana taimako kaiwa ga mutane dubu dari bakwai da hamsin, wadanda kusan rabinsu yara ne da tashin hankalin na Mozambique ya raba da muhallansu a cikin kasar.

Hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ba za ta iya kai wa ga bakwai daga cikin larduna goma sha shida na Cabo Delgado ba saboda matsalar rashin tsaro.

Domin yakar masu tayar da kayar bayan gwamnatin Mozambique ta gayyaci masu bayar da shawara na rundunar sojin Amurka kan su taimaka mata.

Yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Mozambique din da gwamnatin Amurka ita ce sojojin Amurkar za su horad da dakarun yankin da ke yakar ‘yan bindigar.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
An kafa sansanonin wucin-gadi ga dubban ‘yan gudun hijira da rikicin ya raba da muhallansu

Shi dai wannan yanki daman ya dade da matsalar tsaro, amma tashin hankali na hare-haren masu ikirarin jihadi ya fara ne a shekara ta 2017.

Ana ganin wasu mayaka da ke da alaka da kungiyar al-Shabab a yankin na da alaka da kungiyar IS, mai da’awar kafa daular Musulunci.

Sannan katutun fatara da talauci da rikice-rikice a kan mallakar gonaki da filaye da kuma rashin aikin yi sun taimaka wajen fada a tsakanin jama’a.

Cabo Delgado wuri ne mai muhimmanci ga gwamnati, wanda kuma dalilan da ke haddasa sabani da fadace-fadace a tsakanin al’ummomin yankin, wanda wuri ne mai arzikin iskar gas, da gwamnati ke haka da hadin kan kamfanonin kasashen.

(BBC Hausa)

More News

Mutane uku sun mutu a ruftawar wani ginin bene a Kano

Hukumar Bada Agajin Gaggawa Ta Ƙasa NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane uku bayan da wani bene mai hawa uku ya ruguzo a unguwar...

Ganduje Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Shirya Zanga-Zangar Neman A Sauke Shi

Shugaban jam'iyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin jihar Kano ta jam'iyar NNPP ita ce ke da alhakin shirya zanga-zanga iri...

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...