Matsalar Tsaro Na Barazana Ga Hadin Kan Najeriya | VOA Hausa

Wata budaddiyar wasika da tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya aikawa shugaba Muhammadu Buhari, ta nuna damuwa matuka kan yadda matsalar tsaro ke barazana ga Najeriya a matsayinta na kasa daya.

Wasikar wacce aka wallafa a jaridun Najeriya da dama a yau Litinin, ta yi bayani kan dumbin matsalolin da ke addabar kasar, amma ta fi mayar da hankali ne kan batun tsaro.

A wasikar, Obasanjo ya ce, duk da cewa ana ci gaba da fuskantar matsalar Boko Harm gwamnatin na ikirarin cewa tana samun nasara akansu.

Obasanjo ya ce ba wani nasara da ake samu musamman in an duba yadda har yanzu mayakan Boko Haram ke nuna karfin su, kuma suna ci gaba da ta da tarzoma a shiyyar arewa maso gabas, al’amarin da ke wofintar da ikirarin gwamnatin Buhari.

Cif Obasanjo ya kuma kara da cewa maganar da babban hafsan hafsoshin sojojin Najeriya ya yi inda ya ce, sojoji ba su da kwazo da himmar yin yaki, abin da ke jawo kalubale wajen cin galaba Boko Haram, wannan wata babbar shaida ce ta kasawar gwamnatin.

Matsalar rikicin manoma da makiyaya da abin ya faro kamar wasa da kuma
gwamnati ta yi maganar rikon sakainar kashi, sannu a hankali ta rikide zuwa aikaaikar ‘yan bindiga, da garkuwa da mutane dan neman kudin fansa, ga kuma fashi da makami.

Abin bakin ciki ne inji Obasanjo yadda ake daukar Fulani makiyaya ne ke tafka wannan aikaaika. Sannan wasu ‘yan Najeriya da abokan Najeriyar ke ganin cewa shugaba Buhari a matsayinsa na bafulatani, ya ce hakan abin bakin ciki ne.

Obasanjo ya kawo misali da kisan kare dangin da ya auku a kasar Rwanda, inda ya ce, barin kasar a hannun tsageru suna daukan doka a hannunsu, zai iya jefa Najeriya “cikin kangin kisan kare dangin da aka gani a Rwanda wanda ake tunanin ba zai faru ba sai kuma ga shi ya faru.”

Daga dukkan alamu wasu kwararru a Najeriya irinsu Dr. Kabiru Adamu, sun amince da wasu daga cikin kalaman tsohon shugaban kasar inda ya ce lallai matsalar tsaro a Najeriya sai ta’azzara take a kusan duka sassan kasar
wanda a halin yanzu ma sai karuwa take yi fiye da a baya.

Shi ma tsohon gwamnan mulkin soja na jihohin Kano da Binuwai, Kanar
Aminu Isa Kontagora, ya ce Obasanjo a matsayinsa na dattijon kasa da ya
shugabanci kasar, dole ne a saurara masa, domin yana da hujjojin yin
wannan korafi.

More News

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miĆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaĆ™i da yiwa tattalin arzikin Ć™asa ne ya hana shi bayyana...