Matatar Mai Ta Dangote Za Ta Fara Sayo ÆŠanyen Man Fetur Daga Kasar Amurka

Matatar man fetur ta Dangote ta shirya sayo É—anyen man fetur daga kasar Amurka.

A cewar wani rahoton jaridar kasuwanci ta Bloomberg cinikayyar da aka ƙulla ta sayen man ya nuna yadda ɗanyen mai na kasar Amurka ke gogayya a kasuwar duniya.

Rukunin kamfanin Trafigura Group ya sayarwa da matatar ta Dangote É—anyen man fetur nau’in West Texas Intermediate da za a kai matatar a Æ™arshen watan Faburairu kamar yadda wasu majiyoyi suka fadawa jaridar.

Wannan ne dai karo na farko da babbar matatar man fetur ɗin take sayan ɗanyen mai wanda ba daga Najeriya aka haƙo shi ba.

Amma kuma ƴan kasuwar dake harkar ɗanyen mai sun gaza bai yana dalilin da yasa matatar mai dake cikin ƙasa mai cike da arzikin mai za ta riƙa sayo ɗanyen man fetur daga kasar Amurka inda suka ke ganin cewa hakan baya rasa nasaba da farashi.

More News

Ƴan sanda sun kama mutane 50 kan rikicin da ya faru a wata kasuwa a Lagos

Rundunar Æ´an sandan jihar Legas ta kama mutane sama da 50 da ake zargin suna da hannu rikicin da ya faru a kasuwar Ile...

Ƴan Sanda sun kama wanda ya shirya kai harin jirgin ƙasar Abuja-Kaduna a shekarar 2022

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Abdullahi wanda ake zargi da kitsa harin jirgin ƙasar da...

Ƴansanda sun kama wanda ya kitsa harin da aka kai wa jirgin ƙasa a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a ranar Alhamis, ta sanar da kame wanda ake zargin ya shirya harin da aka kai a jirgin ƙasan Abuja-Kaduna...

Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani É“angare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane...