Matashi mai fasaha ya roƙi Ganduje da ya cika masa alƙawarin da ya yi masa na N5m

Matashi mai fasaha Faisal ya roƙi Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje da ya cika alƙawarin da ya yi masa na ba shi tallafi don inganta fasaharsa.

Matashin dai ya yi wannan kira ne a shafinsa na Facebook a yau Laraba.

Ga abin da ya ke cewa:

Ni faisal sunusi mika’il (faisalart) ina rokon maigirma gwannan jahar kano Dr abdullahi umar ganduje daya Cika alkawarin dayai min Na naira million biyar.

A Lokacin da gwamnatin jahar kano tayi kirana gidan gwamnati don nunawa maigirma gwannan jahar kano Dr abdullahi umar ganduje irin fasahar da Allah ya bani wadda cikin ikon Allah nakera babur mai kafa uku wanda ake kira adaidaita sahu wanda ninayi design dinsa kuma nakerashi da hannuna

maigirma gwanna da mataimakin gwamna da sauran commissioners suka duba mashin din sosai suka yaba kuma sukai alfahari gwanna da mataimakin sa Dr.nasuru yusuf gawuna suka shiga nakewaya dasu a mashin din

Bayan haka sai maigirma gwannan jahar kano Dr abdullahi umar ganduje yamin alkawarin gwamnatin jahar kano zata bani kyautar naira million biyar don bunkasa fasahata ta kere kere a ranar 8 ga watan February 2023

Yau kimanin wajen wata hudu kenan kudin basuzo gareni ba, ina rokon maigirma gwannan jahar kano Dr abdullahi umar ganduje daya Cika alkawarin dayai min

More News

Ƴan sanda sun kama mutane 50 kan rikicin da ya faru a wata kasuwa a Lagos

Rundunar ƴan sandan jihar Legas ta kama mutane sama da 50 da ake zargin suna da hannu rikicin da ya faru a kasuwar Ile...

Ƴan Sanda sun kama wanda ya shirya kai harin jirgin ƙasar Abuja-Kaduna a shekarar 2022

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Abdullahi wanda ake zargi da kitsa harin jirgin ƙasar da...

Ƴansanda sun kama wanda ya kitsa harin da aka kai wa jirgin ƙasa a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a ranar Alhamis, ta sanar da kame wanda ake zargin ya shirya harin da aka kai a jirgin ƙasan Abuja-Kaduna...

Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani ɓangare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane...