Hajiya Nana, uwargidan mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, a ranar Laraba, ta jagoranci tawagar shugabannin mata na Renewed Hope Initiative a ziyarar hadin kai da suka kai a sakatariyar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta kasa a Abuja.
Tawagar ta hada da uwargidan kakakin majalisar wakilai, Hajiya Fatima; uwargidan shugaban majalisar dattawa, Ekaette Akpabio; uwargidan shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin kasar Salamatu Gbajabiamila da matan ministoci da dama a gwamnatin mai ci.