Mata 48 da Boko ta sace a Borno sun shaƙi iskar ‘yanci bayan sun kwashe kwanaki a hannun ƴan ta’addar

Kauyukan Maiwa da Shuwarin da ke karamar hukumar Mafa ta jihar Borno sun fuskanci harin Boko Haram inda kungiyar ta’addancin ta yi garkuwa da mata kusan 48.

Sai dai ‘yan ta’addan na arewa maso gabas sun bukaci iyalan matan da aka kama su biya kudin fansa naira miliyan 2.4.

An sako su ne bayan an biya kudin fansar.

Zagazola Makama, kwararre a fannin yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a tafkin Chadi, ya tabbatar da sakin nasu.

Makama ya bayyana a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis cewa an sace matan ne a gonakinsu a ranar 22 ga Agusta, 2023.

A ranar Laraba, 23 ga watan Agusta, an sako matan bayan sun biya Naira 50,000 kowannensu a matsayin kudin fansa ga ‘yan ta’adda,” inji Makama.

Jihar Borno dai an kwashe shekaru ana fama da hare-haren ‘yan ta’addan a kan manoma tare da kashe su ko kuma yin garkuwa da su.

More News

An samu ambaliyar ruwa a Adamawa

Anguwan Tana, al’ummar karamar hukumar Yola ta Arewa, sun shiga tasgaro a ranar Alhamis sakamakon ambaliya daga kogin Kilange da kogin Faro. Mazaunan garin...

Sojoji sun ceto mutane 6 daga cikin ɗaliban jami’ar Gusau da aka sace

Sojoji sun ceto dalibai mata shida daga cikin daliban Jami'ar Gwamnatin Tarayya dake Gusau da aka bada rahoton yan bindiga sun yi garkuwa da...

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da ɗaliban Jami’ar Tarayya da ke Gusau

An sace wasu daliban jami’ar tarayya ta Gusau da ba a tantance adadinsu ba da sanyin safiyar Juma’a. ‘Yan ta’addan masu yawan gaske sun...

Ƴan sanda sun kama masu safarar makamai wa ƴan bindiga

Jami’an hukumar ‘yan sanda reshen Karasuwa a jihar Yobe sun cafke wasu mutane biyu da ake zargi da kai wa ‘yan bindiga makamai da...