Masu zanga-zanga sun yanke hulda da gwamnatin Sudan|BBC Hausa

Masu zanga-zanga a Sudan sun ci gaba da gwagwarmaya

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Shugabannin masu zanga-zanga a Sudan sun ce ba su ba gwamnatin soja ta kasar wadda ta maye gurbin hambararren shugaba Omar al-Bashir.

Suna zargin gwamnatin tana dauke da sauran mambobin tsohuwar gwamnatin al-Bashir.

Dubban masu zanga-zangar sun mamaye harabar ma’aikatar tsaro ta kasar a birnin Khartoum domin tataunawa gabanin sanarwar wata sabuwar gwamnati ta farar hula da suke o ta karbi ragamar mulki daga hannun gwamnatin sojin kasar.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Wasu masu zanga-zanga a birnin Khartoum

A nata bangaren kuwa, gwamnatin sojin ta ce a shirye take ta mika mulki, amma ta fi so a yi hadin gambiza, wato a kafa gwamnatin sojoji da fararen hula.

Amma kakakin masu zanga-zangar Mohamed al-Amin ya ce sun dawo daga rakiyar majalisar sojojin da ke mulkin kasar, kuma suna kallonta a matsayin “wani bangare na tsohuwar gwamnatin” kuma su sha alwashin ci gaba da gwagwarmaya har sai sun cimma bukatunsu.

More News

Mutane uku sun mutu a ruftawar wani ginin bene a Kano

Hukumar Bada Agajin Gaggawa Ta Ƙasa NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane uku bayan da wani bene mai hawa uku ya ruguzo a unguwar...

Ganduje Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Shirya Zanga-Zangar Neman A Sauke Shi

Shugaban jam'iyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin jihar Kano ta jam'iyar NNPP ita ce ke da alhakin shirya zanga-zanga iri...

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...