Masu binciken sun gano maganin cutar so – Arewa News

Hoton zuciyar da aka mannawa bandeji

Hakkin mallakar hoto
eternalcreative via Getty Images

— BBC Hausa

Wani mai bincike ya ce ya samo hanyar da za a magance damuwar da ke biyo bayan rabuwa da masoyi ta hanyar bayar da shawarwari da lallami da kuma shafe tunanin wannan masoyin.

Dakta Alain Brunet, ya shafe fiye da shekara 15 yana nazari a kan irin damuwar da ke biyo bayan rabuwa da masoyi ko masoyiya inda ya yi aiki tare da kwararru kan soyayya da kuma wadanda suka taba shiga irin wannan matsala.

A binciken nasa dai ya fi mayar da hankali a kan yadda za a lallashe shi tare da bayar da shawara ga wanda ya shiga matukar damuwa bayan rabuwa da masoyi/masoyiya.

A cikin binciken nasa ya gano cewa kwayar propranolol , ita ce kwaya mafi dacewa da mutum zai yi amfani da ita wajen maganin hawan jini da ciwon zuciya da ciwon kai mai tsanani idan ya tsinci kansa a cikin damuwar so.

  • ‘Matan Najeriya ba su iya soyayya kamar Turawa ba’
  • Soyayyar shafukan sada zumunta? Ga hanyoyi bakwai na samun nasara

A tsarin bayar da shawarwari, idan mutum ya samu kansa a cikin ciwon so, ana so mutumin ya fara shan kwayar Propranolol awa daya kafin a fara bashi shawarar da kuma lallashi.

Idan aka zo wajen bayar da shawarar, akan fara sa mutum ya rubuta irin abin da ke damunsa, sannan kuma ya karanta da karfi idan ya kammala rubutun.

Wani likitan kwakwalwa dan kasar Canada, ya shaida wa BBC cewa, ” irin wannan karatu da karfi zai sa mutum kwakwalwarsa ta bude sosai, sannan kuma idan akwai abin da ya manta zai iya tunawa”.

Irin wannan tsari wata dama ce ga wanda ya tsinci kansa cikin wannan matsala ya samu sauki a kan abin da ke damunsa.

Dr Brunet ya ce ” Muna amfani da wannan hanya wajen fahimtar ya yanayin matsalar mutum ta ke, ta ina za a fara magance ta da kuma yadda mutum zai manta da duk wata damuwar soyayyar da ya shiga”.

Hakkin mallakar hoto
Rex Features

Image caption

Kate Winslet da Jim Carrey ma’aurata ne wandada yanzu kuma sun manta da juna

Yawanci kwakwalwa na rike abubuwa da dama kamar abubuwa na hakika, amma kuma abin tausayi ko na ban haushi shi ma kwakwalwa kan rike shi sosai.

Kwayar propranolol na taimakawa matuka gaya wajen rage radadin damuwar so ko tunanin abubuwan da suka faru a lokacin da mutum ke kan ganiyar soyayya.

Dakta Brunet ya ce a binciken da ya yi, za a iya samun kaso 70 cikin 100 na mutanen da suka shiga cikin damuwar so da za su warke ta hanyar basu shawarwari akai-akai amma ba sai an dauki dogon lokaci ba.

A kwanakin baya-bayannan, likitan ya kaddamar da wani shiri a Faransa wanda ya taimaka wajen farfado da wadanda mummunan harin nan na birnin Paris ya rutsa da su.

Ya taimaka wa wadannan mutanen ne ta hanyar ba wa wasu likitoci 200 horo na musamman a kan yadda za su rinka kula da irin mutanen da harin ya rutsa da su inda ya koyar da su yadda za su rinka ba su shawarwari da lallami da dai sauran dabaru domin mantawa da wani mummunan abu da ya samu mutu.

Ya zuwa yanzu, an yi wa fiye da mutum 400 maganin damuwarsu ta hanyar lallami da shawarwari kamar yadda Dakta Brunet ya tsara.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Dakta Alain Brunet ya yi aiki ne tare da wanda ya kirkiri kwayar propranolol domin gano maganinta da kuma illarta

Image caption

Dakta Brunet na fatan ya yi wa masu tsoron wani abu magani

Dakta Brunet ya ce, wasu da suka tsinci kansu a irin wannan matsala, sukan halarci wajen bayar da shawarwari sau biyar kafin su warke daga ciwon so, ma’ana kafin su manta da damuwar da suke ciki ko kuma su daina tunanin da suke yi a kan masoyi/masoyiya.

A yanzu haka Dakta Brunet na da ma’aikatan da ke taimaka masa wajen warkar da wadanda suka fada cikin kogon so guda 60, kuma yawancinsu wadanda suka warke ne daga irin wannan cuta ta ciwon so.

Ya ce yana fata zai fadada wajen bayar da shawarwarinsa tare da fadada ayyukansa nan ba da jimawa ba.

More News

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...