Masar ce za ta karbi bakuncin Gasar Cin Kofin Afirka a 2019

The Africa Cup of Nations trophy

Wannan karo na biyar da Masar za ta karbi bakuncin gasar

Kasar Masar ce za ta karbi bakuncin Gasar Cin Kofin Kasashen nahiyar Afirka a bana, kamar yadda hukumar da ke kula da harkokin kwallon kafa a nahiyar wato Caf ta bayyana.

Masar ta doke kasar Afirka Ta Kudu, wadda ita ce kasa daya tilo da ta kalubalence ce ta, a wani taron kwamitin zartarwa da aka yi.

Tun da farko an tsara cewa kasar Kamaru ce za ta karbi bakuncin gasar a bana, amma sai aka karbe daga hannunta a watan Nuwambar bara saboda yadda take tafiyar hawainiya wurin gudanar da shirye-shiryen.

Wannan ne karo na biyar da kasar Masar za ta karbi bakuncin gasar, kuma tana da watanni shida kawai kafin fara gasar, wadda a bana kasashe 24 ne za su halarta.

Za a fara gasar ne a watan Yunin bana.

Tun a baya dai hukumar ta Caf ta bai wa kasar Kamaru damar karbar bakuncin gasar shekaru biyu da suka gabata, kuma hakan na nufin an dakatar da wadanda za su karbi bakuncin gasar a shekarun 2021 da 2023 daga shirye-shiryensu.

Yanzu dai hukumar za ta sanar da wadanda za ta karbi bakuncin gasar a ranar Laraba 9 ga watan Janairu.

Kasar Ivory Coast da kuma Guinea wadanda su ne tun farko aka tsara za su karbi bakuncin gasar a 2021 da kuma 2023 sun nuna rashin jin dadinsu da hukuncin da kotun sulhu mai kula da harkokin wasanni ta dauka,

Daga nan, ne sai Guinea ta yanke shawarar dakatar da neman shirya gasar har sai a shekarar 2023.

An sanar da wannan hukunci ne a babban birnin kasar Senegal wato Dakar, wanda a ranar Talata ake sa ran zai karbi bakuncin bikin shekara-shekara inda ake bayar da kyautuka ga gwarazan ‘yan kwallo.

Dan wasan kasar Masar Mohamed Salah na shirin kare kambunsa yayin da zai kara da Pierre-Emerick Aubameyang na kasar Gabon da kuma Sadio Mane na kasar Senegal a matsayin gwarzon dan kwallo na bana.

More News

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miĆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaĆ™i da yiwa tattalin arzikin Ć™asa ne ya hana shi bayyana...