Manchester United ta tuntubi Ernesto Valverde tsohon kocin Barcelona

Ernesto Valverde

Asalin hoton, Getty Images

Manchester United ta tuntubi tsohon wanda ya horar da Barcelona, Ernesto Valverde, domin masa tayin aikin kocin kungiyar.

Mai shekara 57 yana daga cikin wadanda United ke zawarci, domin maye gurbin Ole Gunnar Solskjaer zuwa karshen kakar nan, kafin ta tantance wanda za ta bai wa aikin wuka da nama.

Ita dai United ta mayar da hankali kan daukar kocin rikon kwarya, domin taga kamun ludayi kafin ta kulla yarjejeniya mai tsawo da duk wanda za ta dauka.

Kungiyar ta Old Trafford na ganin da kyar ne idan za ta samu daukar mai horar da Paris St Germain, Mauricio Pochettino, wanda ya yi kocin Southampton da kuma Tottenham a gasar Premier League.

Aikin koci na karshe da Valverde ya yi shine a Barcelona, wadda ta koreshi a Janairun 2020, duk da kai kungiyar lashe La Liga da kuma Copa del Rey a 2018.

Ya kuma lashe kofi uku a babbar gasar Girka tare da Olympiakos ya kuma ja ragamar Espanyol da Valencia da Athletici Bilbao, wadda ya ja ragamar wasa sama da 300 a karo biyu da ya horar da kungiyar.

Valverde bai taba aiki da wata kungiyar Ingila ba, kuma baya harshen Turanci.

United ta bai wa Michael Carrick aikin rikon kwarya, wanda ya ja ragamar kungiyar ta doke Villareal 2-0 a Champions League ranar Talata ta kuma kai zagayen gaba a gasar.

Ranar Lahadi United ta sallami Solskjaer, bayan da Watford ta casa ta 4-1 a wasan mako na 12 a gasar Premier League ranar Asabar.

More News

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miĆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaĆ™i da yiwa tattalin arzikin Ć™asa ne ya hana shi bayyana...