
Wasu majiyoyi sun bayyana cewa an kama shine ranar Talata kan wata huduba da ya yi inda a ciki ya zargi gwamnatin shugaban kasa Muhammad Buhari da yin ko in kula kan yadda sha’anin tsaro ya tabarbare a sassa daban-daban na kasarnan.
Wakilin jaridar Daily Trust ya gano cewa,Abu Ammar na tare da abokinsa mai suna Mallam Shamsu lokacin da aka kira shi a waya aka bukaci da ya kai kansa ofishin hukumar DSS na jihar.
Malamin ya amsa gayyatar inda suka tafi tare da Shamsu zuwa ofishin amma daga bisani sai suka ce abokin nasa ya dawo gida shi kuma suka cigaba da tsare shi.
Murtala ɗa ne ga malamin ya tabbatarwa da wakilin jaridar tsare mahaifinsa lokacin da wakilin ya ziyarci gidansu dake Filin Samji a Katsina.