Majalisar dokokin jihar Kano ta yi sabon mataimakin shugaba

Majalisar dokokin jihar Kano, ta zabi Kabiru Hassan Dashi mamba mai wakiltar mazabar Kiru a matsayin sabon mataimakin kakakin majalisar.

Zaben Dashi da aka yi ya biyo bayan murabus da mataimakin kakakin majalisar Zubairu Hamza Masu yayi.

A kwanakin baya ne Masu wanda shi ne ke wakiltar al’ummar Sumaila a majalisar ya sauya sheka daga jam’iyar APC zuwa NNPP.

Dashi ya kasance shugaba da kuma mataimakin masu rinjaye na majalisar, ya yadda ya zama mataimakin shugaban majalisar biyo bayan amincewa da 28 cikin 40 na mambobin majalisar da suka yi.

More from this stream

Recomended