Majalisar Dattawa ta tsige Ndume a matsayin babban mai tsawatarwa

Majalisar dattawa ta tsige Sanata Mohamed Ali Ndume (Borno ta Kudu) a matsayin babban mai tsawatarwa, inda ta maye gurbinsa da Sanata Tahir Mungono (Borno North).

An yanke hukuncin ne ta hanyar kuri’ar murya da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya jagoranta yayin zaman majalisar na ranar Laraba.
 
Wannan mataki dai ya biyo bayan sukar da Ndume ya yi a baya-bayan nan ga gwamnatin shugaba Bola Tinubu, wanda ya bayyana a matsayin “kakistocracy” – tsarin da mafi karancin kwarewa da cin hanci da rashawa ke rike da madafun iko.
 
Ndume ya kuma soki manufofin gwamnati na baya-bayan nan, ya kuma bukaci shugaban kasar da ya kewaye kansa da kwararrun mutane.
 
A martanin da ya mayar, shugabannin jam’iyyar APC na kasa sun bukaci Ndume ya yi murabus daga jam’iyyar ya koma jam’iyyar adawa.

More from this stream

Recomended