Majalisar Dattawa Ta Dakatar Da Sanata Abdul Ningi

Majalisar Dattawa ta dakatar da sanata Abdul Ningi kan zargin da ya yiwa cewa an yi cushen naira tiriliyan 3.7 a cikin kasafin kuɗin shekarar 2024 da majalisar ta zartar.

Ningi ya bayyana haka ne a cikin wata hira da yayi da kafar yaɗa labarai ta BBC Hausa inda ya ce Kungiyar Sanatocin Arewa za ta tattauna da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio da kuma shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu kan batun.

A yayin zaman majalisar na ranar Talata, Sanata Adeola Solomon daga jihar Ogun shi ne ya gabatar da kuɗiri inda sanatoci suka tattauna kan zargin kuɗirin ya samu goyon bayan Sanata Ned daga jihar Edo.

Bayan doguwar muhara Sanata Jimoh Ibrahim daga jihar Edo ya bada shawarar da a dakatar Ningi na tsawon watanni.

Amma da yake tofa albarkacin bakinsa kan batun Sanata Asuquo Ekpeyong daga jihar Cross Rivers ya roƙi a rage tsawon dakatarwa zuwa watanni shida.

Amma kuma Sanata Sani Musa daga jihar Niger ya nemi a dakatar da Ningi har tsawon watanni uku sannan a saka shi ya rubuta wasikar bada hakuri.

A ƙarshe shugaban majalisar Sanata Akpabio ya amince a dakatar da Ningi na tsawon watanni uku.

More from this stream

Recomended