Mahaifin Messi ya tattauna da Manchester City kan ɗansa, Koeman ya ce ba ya buƙatar Suarez a Barcelona

Lionel Messi in a Barcelona shirt

Jaridar Sun ta ruwaito cewa mahaifin Lionel Messi yana Ingila inda yake tattaunawa da Manchester City wacce za ta bai wa dansa kwangilar shekara biyu bayan wasan na Argentina, mai shekara 33, ya ce yana son barin Barcelona.

Idan komai ya tafi kamar yadda ake so, City za ta biya £500m kan dan wasan, in ji Telegraph.

Messi zai halarci atisaye a filin wasan Barcelona ranar Litinin domin guje wa matakin shari’a da kungiyar za ta iya dauka a kansa. (Sport – in Spanish)

Manchester United tana da kudin sayen Messi, sai dai har yanzu tana zawarcin dan wasan Borussia Dortmund da Ingila Jadon Sancho, mai shekara 20, a cewar Express.

Sabon kocin Barcelona Ronald Koeman ya gaya wa dan wasan Uruguay Luis Suarez, mai shekara 33, cewa ya nemi wata kungiyar domin ba ya bujatarsa a Barca. (Mail)

An ba da dama ga dan wasan Bournemouth da Wales David Brooks, mai shekara 23, ya tafi zaman aro kuma akwai yiwuwar Manchester United ta dauko shi idan ta gaza biyan £108m kan Sancho. (Express)

Monaco ta ki amsa tayin Manchester United na biyanta £22m don karbo dan wasan Faransa Benoit Badiashile, mai shekara 19. (RMC via Star)

Tottenham na dab da kammala kulla yarjejeniya da Wolverhampton Wanderers don dauko dan wasanta Matt Doherty. Wolves na so a ba ta kusan £20m kan dan wasan mai shekara 28 dan kasar Jamhuriyar Ireland sai dai Tottenham na son biyan kasa da haka. (Independent)

More News

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...