Mahaifin gwamna Soludo ya mutu yana da shekaru 92

Gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo ya yi rashin mahaifinsa, Simeon Nwankwo Soludo, (Ichie Akukananwa 1). a ranar Litinin

Marigayin ya mutu yana da shekaru 92 a duniya

Mai magana da yawun gwamnan, Christian Aburime a wata sanarwa ya ce Pa Soludo ya mutu da tsakar daren ranar Litinin bayan gajeruwar rashin lafiya.

A cewar sa Pa Soludo ya mutu ya bar ƴaƴa maza 7 da matayensu su 8, jikoki 22 da kuma tattaba kunne guda 6.

More from this stream

Recomended