Mafi kankantar Albashi: Malaman makaranta sun koka a Kano

Ganduje

Hakkin mallakar hoto
Salihu Tanko Yakasai

Wasu malaman makarantun firamare a jihar Kano sun ce ba su gani a kasa ba dangane da bugun-kirjin da gwamnatin jihar ke yi cewa ta fara aiwatar da sabon tsarin albashi mafi kankanta na naira dubu talatin.

Malaman dai na zargin cewa rage musu tsohon albashin aka yi maimakon kari.

Wani malami ya shaida wa BBC cewa “mun ji an ce an samu karin amma ni rabin nawa na da na samu saboda haka ina kira ga gwamnati da ta duba yanayin da muke ciki ta yi abin da ya kamata.”

Ita ma wata malama ta ce “suna ta cin burin sayen mota amma sai ga shi naira 3000 kawai ta gani a kan albashin nata.”

To sai dai kungiyoyin kwadago sun ce sun fara tattauna wa da mahukunta domin shawo kan matsalar.

Shugaban kungiyar kwadago na jihar Kano, Comrade Kabiru Minjibir ya ce sun samu labarin korafin malaman makarantar kuma ya ce suna duba hanyar warware matsalar.

Ita ma gwamnatin jihar Kano, ta bakin Murtala Sule Garo, kwamishinan kananan hukumomi, ta ce ita ma tana kokarin gano abin da ya jinkirta biyan malaman makarantun Firamare sabon albashin.

Sabanin yadda a wasu kasashe da dama a duniya ake fifita malaman makaranta, kasancewarsu ginshiki ga ci gaban al`umma, a Najeriya malaman makaranta, musamma kananan makarantu na kukan cewa ana mai da su `ya`yan bora.

Sun yi zargin cewa a wasu matakan ana hana su ko kuma a jinkirta ba su wasu hakkokinsu, saboda kallon da ake musu cewa sun yi yawa.

Amma masu lura da al`amura na cewa idan ba a musu kari ba, to bai kamata a hana su hakkinsu ba.

More News

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...