Ma’akacin Hukumar Alhazai Ya Mayar Wa Gwamnati Rarar Kudin Da Ya Saura

Wani jami’in hukumar alhazai mai suna Muhammad Salish Abubakar mai kula da karamar hukumar Rijau, ya ce bayan ya rabawa Alhazan 75 da ke karkashinsa kudin guzirin dalar Amurka 800, sai ya ga yana da rarar dala dubu 20 (kimanin Naira Miliyan 8 na kudin Najeriya), Shi ne ya dawo da kudin a ofishin Hukumar Alhazan jihar ta Neja saboda, a cewarsa, ba hakkinsa bane.

Hukumar Alhazan jihar Nejan ta nuna jin dadi tare kuma da yaba wannan matakin ta kuma bashi takardar yabo ta Musamman kamar yadda Daraktan Ayyuka na hukumar Malam Attahiru Bala Dukku ya tabbatar,

A halin da ake ciki kuma, hukumar Alhazan Nigeria ta kai kara a kotu domin bin kadin mutuwar wani alhajin jihar da ya fado daga saman Na’urar kai mutane saman bene ya mutu a aikin hajjin da ya gabata bisa ga bayanin mukaddashin sakataren hukumar jin Dadin Alhazan jihar Neja Umar Makun Lapai.

Yanzu dai hukumar Alhazan tace ta bude kofar biyan kudin kujerar aikin Hajji mai zuwa da za a kai Naira Miliyan daya a Banki, ta kuma gargadi maniyyata kada su ba wani jami’in hukumar kudi a hannu.

Saurari cikakken rahoton Mustapha Nasiru Batsari.

More News

Buhari ya rantsar da sabon Alkalin Alkalai

Shugaban kasa, Muhammad Buhari ya rantsar da mai shari'a, Olukayode Ariwoola a matsayin, babban Alkalin Alkalai na Najeriya. Hakan na zuwa ne biyo bayan murabus...

‘Kyale kowa ya mallaki makami a Zamfara na da haɗari’

Masana a harkar tsaro sun bayyana cewa matakin da gwamnatin jihar Zamfara da ke Najeriya ta dauka na kyale farar-hula su mallaki bindiga yana...

Hotunan Daurin Auren Dan Gwamnan Nasarawa

Manyan baki da dama ne ciki har da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo suka halarci daurin auren dangidan gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule da...

Hotunan Daurin Auren Dan Gwamnan Nasarawa

Manyan baki da dama ne ciki har da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo suka halarci daurin auren dangidan gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule da...