Liverpool ta kasa dalewa teburin Firimiya

Liverpool

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Liverpool ta barar da damar dare wa teburin Premier bayan Everton ta rike ta babu ci a Goodison Park.

Liverpool za ta ci gaba da zama matsayi na biyu bayan ta gaza doke Everton inda suka tashi wasa 0-0 a ranar Lahadi.

Tazarar maki daya ne Manchester City da ke saman teburin gasar ta ba Liverpool.

City ta doke Bournemouth ne 1-0 a ranar Asabar, inda take da maki 71, yayin da Liverpool ke da maki 70.

Yanzu hamayya kan wanda zai lashe kofin Premier ta dawo ne tsakanin Manchester City da Liverpool yayin da ya rage wasanni tara a kammala gasar.

Chelsea ta doke Fulham

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Gonzalo Higuain ne ya fara ci wa Chelsea kwallo a raga

Chelsea ta doke Fulham ne ci 2-1, inda yanzu wasa 18 ke nan da Chelsea ke doke Fulham a gasar Premier.

Gonzalo Higuain ne ya fara ci wa Chelsea kwallo a raga kafin Jorginho ya kara bayan Chambers ya farke kwallon da Higuain ya fara ci.

Fulham ta sha kashi a wasa takwas cikin tara da ta buga, kuma yanzu tazarar maki 10 ya raba da ta kasan tebur yayin da ya rage wasa tara a karkare Premier.

More News

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miĆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaĆ™i da yiwa tattalin arzikin Ć™asa ne ya hana shi bayyana...