Kungiyar Likitoci reshen Jihar Kaduna (ARD), a ranar Alhamis, ta gudanar da zanga-zangar lumana domin neman a sako abokin aikinsu, Dokta Ganiyat Popoola ba tare da wani sharadi ba da aka yi garkuwa da ita a ranar 27 ga Disamba, 2023 a gidanta da ke Kaduna.
An yi garkuwa da Dr. Popoola tare da mijinta da kuma dan uwanta, amma an sako mijinta bayan ya shafe makonni a tsare, inda ya bar matarsa mai shayarwa a tsare sama da watanni takwas.
Da yake jawabi ga manema labarai a karshen zanga-zangar lumana da ta gudana a harabar cibiyar kula da ido ta kasa a Kaduna, shugaban kungiyar ARD a jihar Kaduna, Dokta Muhammad Okpanaki ya ce, idan ba a biya musu bukatarsu ta gaggawar shiga tsakani da sakin abokin aikin nasu ba, sun ce ba su da wani zaɓi sai dai su yi yajin aikin don biyan bukatunsu.