Likitoci a Zamfara sun janye yakin aiki

Likitoci a asibitin kwararru na Yariman Bakura, AYBSH, Gusau a Zamfara sun dakatar da shirinsu na shiga yajin aikin sai baba-ta-gani a ranar 4 ga watan Satumba.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kungiyar likitocin Najeriya reshen jihar NMA ta fitar a ranar Juma’a mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar na jiha, Dakta Sanusi Bello da sakataren kungiyar, Dakta Murtala Shinkafi.

Ku tuna cewa likitocin sun sanya ranar 4 ga watan Satumba su fara yajin aikin sai baba-ta-gani kan rashin biyansu albashi da alawus alawus da gwamnatin jihar ta yi.

Likitocin sun bayyana cewa gwamnatin jihar ta warware rikicin ma’aikatan cikin ruwan sanyi wanda hukumar NMA ta jihar ta gamsu.

More News

Mutane uku sun mutu a ruftawar wani ginin bene a Kano

Hukumar Bada Agajin Gaggawa Ta Ƙasa NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane uku bayan da wani bene mai hawa uku ya ruguzo a unguwar...

Ganduje Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Shirya Zanga-Zangar Neman A Sauke Shi

Shugaban jam'iyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin jihar Kano ta jam'iyar NNPP ita ce ke da alhakin shirya zanga-zanga iri...

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...