Lakurawa sun kashe mutane 15 a Kebbi

Aƙalla mutane 15 aka tabbatar da mutuwarsu a wani hari da sabuwar ƙungiyar ƴan ta’adda ta Lakurawa ta kai ƙauyen Mera a ƙaramar hukumar Augie ta jihar Kebbi.

A zantawar da ya yi ta wayar tarho da jaridar The Cable a ranar Asabar, Nafiu Abubakar mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Kebbi ya ce an kai harin ne da misalin ƙarfe biyu na ranar Juma’a.

“Ƴan ta’addar sun farma ƙauyen misalin ƙarfe biyu na ranar Juma’a,” Abubakar ya ce ya kuma ƙara da cewa adadin shanu masu yawan gaske suka yi gaba da su a yayin harin.

“Bincike na cigaba da gudana kuma za a sanar da al’umma sakamakon,”

An binne mutanen a ranar Asabar bayan yi musu jana’iza da ta samu halartar fitattun mutane da suka haɗa da Abubakar Tafida mataimakin gwamnan jihar Kebbi, Sarkin Argungu, Sama’ila Mera da kuma kwamishinan ƴan sandan jihar.

A makon da ya wuce ne ma’aikatar tsaron na Najeriya ta fitar da sanarwar ɓullar ƴan ta’addar na Lakurawa a wasu ƙananan hukumomin jihar Sokoto da Kebbi.

More from this stream

Recomended