Labarai A Takaice

Sarakuna a jihar Zamfara da ke fama da kalubalen tsaro sun bukaci sojoji su je yankin Dunburum a karamar hukumar Zurmi don kwance damarar boma-boman da ba su fashe ba biyo bayan ruwan wuta da sojan su ka yi a yankin.*

*Tun farko sarakunan sun fitar da jerin sunayen mutane mutum 11 wadanda ba su da laifin komai da ruwan wutan sojojin ya hallaka su a yankin na Zurmi. Bayan nan ma sun fitar da jerin sunayen mutanen da su ka samu rauni sakamakon hare-haren na sojan saman Najeriya. Don gudun zargin ko suna shakkar nasarar da sojojin ke samu ne a hare-haren, sarakunan sun bukaci a samu masu bincike masu zaman kan su don tabbatar da bayanin hare-haren na sama sun hallaka farar hula ne ba barayi ba.*

*In za a tuna ministan tsaro Mansur Dan Ali ya zargi wasu masu mukaman gargajiya da hannu a lamarin na satar mutane da zubar da jini.*

*Babban birnin Najeriya Abuja ya zama tamkar ranakun karshen mako don yadda ba yawan motoci kan tituna yayin da mabiya addinin kirista ke bukin ranar gicciye. Bankuna da manyan kasuwanin zamani sun kasance a rufe duk da ba a rasa masu tura kaya musamman dangin mangoro, lemo, abarba da karas ke zagayawa don samun ciniki.*

*Yanayin anguwannin tsakiyar Abuja dama kan zama tamkar ba jama’a sosai duk lokacin da a ka aiyana wani hutu don wa imma mutane na hutawa a cikin gida ko kuma sun yi tafiya zuwa garuruwansu na asali don sada zumunci. Matasa da kwana biyu da su ka wuce su ka baiyana da jarkar mai su na saida lita da dan Karen tsada, yanzu sun bace inda a kan samu man a gidajen mai.*

*Allah ya yi wa babban limamin kasar Ibira a jihar Kogi ta arewa ta tsakiyar Najeriya Imam Musa Galadima rasuwa ya na mai shekaru 98. Limamin dai ya koma ga Allah ne a sanyin safiyar jumma’ar nan 19 ga watan nan na Afrilu.*

*Limamin wanda ya rasu a wani asibiti mai zaman kan sa a Abuja, ya kasance kan mukamin babban limamin ‘yan Ibira na tsawon shekaru 55. Za a yi jana’izar marigayin a garin Okene. Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello wanda shi ma dan kabilar ta Ibira ne ya nuna matukar girgiza da rasuwan limamin ya na mai zaiyana shi da mutum mai tsoron Allah.*

*Masu zanga-zanga a kasar Aljeriya sun fito a jumma’a ta 9 a jere suna masu bukatar murabus din mutum 3 a gwamnatin kasar bayan tun farko shugaba Abdul’aziz Bouteflika ya yi murabus.*

*Duk da ambata ranar 4 ga watan Yuli a matsayin ranar zabe, hakan bai gamsar da masu zanga-zangar ba don su na son duk ‘yan bokon da su ka mamaye mulkin kasar tun samun ‘yanci a 1962 daga Faransa su fice daga gidan gwamnati.*

*Mutum 3 da masu zanga-zanga ke son su sauka daga madafun iko sun hada da shugaban rikwan kwarya Abdelkader Bensalah da shugaban kwamitin tsarin mulkin kasar Tayib Belaiz da kuma mukaddashin firaminista Noureddine Bedoui.*

More News

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...

Sojoji Sun Kashe Mayaƙan IPOB 5

Dakarun rundunar sojan Najeriya da kuma ta rundunar sojan ruwan Najeriya a ranar Talata sun kashe mayaƙan ƙungiyar IPOB guda biyar a yayin musayar...

ÆŠan agajin Izala ya samu lambar yabo, kujerar hajji, kyautar mota bayan ya tsinci naira miliyan 100 ya mayar wa mai su

Salihu AbdulHadi Kankia, mamba ne na kungiyar agaji ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), ya samu yabo da tukuicin mayar da...