Kyari Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Ake Samun Ƙarancin Man Fetur

Shugaban rukunin kamfanonin NNPCL, Mele kyari ya bayyana dalilin da yasa ake sake samun layuka a gidajen mai.

Dogayen layuka sun fara bayyana a gidajen mai a makon da ya wuce hakan ya sa wasu mutane suka fara zargin cewa za a kara kuÉ—in mai.

Amma da yake magana da yan jarida a fadar shugaban kasa Kyari ya alaƙanta ƙarancin mai da cinkoso da ake samu a wasu hanyoyi abin da yasa wasu direbobi suke bi hanyoyi masu nisa domin kaucewa hakan.

Ya kara da cewa ana samar da man fetur kamar yadda ya kamata sosai kuma gwamnatin tarayya tana aiki tuƙuru domin samar da kuɗaden waje a kasuwar musayar kudade domin dai-daita darajar Naira.

More News

Ƴan sanda sun kama mutane 50 kan rikicin da ya faru a wata kasuwa a Lagos

Rundunar Æ´an sandan jihar Legas ta kama mutane sama da 50 da ake zargin suna da hannu rikicin da ya faru a kasuwar Ile...

Ƴan Sanda sun kama wanda ya shirya kai harin jirgin ƙasar Abuja-Kaduna a shekarar 2022

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Abdullahi wanda ake zargi da kitsa harin jirgin ƙasar da...

Ƴansanda sun kama wanda ya kitsa harin da aka kai wa jirgin ƙasa a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a ranar Alhamis, ta sanar da kame wanda ake zargin ya shirya harin da aka kai a jirgin ƙasan Abuja-Kaduna...

Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani É“angare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane...