Kwankwaso da Ganduje: Ko za a yi sulhu?

Yunkurin sulhu a tsakanin tsohon gwamnan jihar Kano Dakta Rabiu Musa Kwankwaso da gwamnan jihar mai ci yanzu Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bar baya da kura.

Tun dai bayan zaben shekara ta 2015 ne dangantaka ta fara tsami tsakanin Kwankwaso da Ganduje da ya yi masa mataimaki a tsawon mulkin shekaru takwas da ya yi a matsayin gwamnan Kano. Sai dai al’amura sun kara dagulewa a tsakanin mutanen biyu, bayan zaben shekara ta 2019. An yi yunkuri ne da ma haduwa ta gaba da gaba a lokacin da gwamnan Kanon Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya je ya yi wa tsohon gwamnan jihar Dakta Rabiu Musa Kwankwaso ta’aziyya a lokacin rasuwar kanin Kwankwason.

Ganduje da Kwankwaso

A hira ta musamman da Uwaisu Abubakar Idris  waikilinmu na Abuja ya yi da tsohon gwamnan Kanon Rabiu Musa Kwankwaso ya tabo batutuwa da dama da suka hadar da batun sauya sheka daga jamiyyarsa ta PDP zuwa APC ko zai sake shiga takarar neman shugabancin Najeriyar a 2023. A cewarsa a yanzu dai ba ya tattaunawa da kowa dangane da batun sauyin sheka, kana batun takara lokaci zai nuna. Haka kuma Kwankwason da ke zaman jagoran siyasar Kwankwasiyya a Najeriya, ya tabo batun rashin tsaro da ake fama da shi musamman a yankin Arewaso maso Yammacin kasar.

More News

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miĆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaĆ™i da yiwa tattalin arzikin Ć™asa ne ya hana shi bayyana...