Kwankwaso ba zai koma APC ba—NNPP

A ranar Asabar din da ta gabata ne jam’iyyar New Nigeria Peoples Party ta yi watsi da fargabar magoya bayanta, inda ta ce dan takararta na shugaban kasa a zaben da ya gabata, Rabiu Kwankwaso, ba zai sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress mai mulki ba.

Jam’iyyar ta mayar da martani ne kan ganawar da Kwankwaso da zababben shugaban kasa, Bola Tinubu suka yi a birnin Paris na kasar Faransa a kwanakin baya, lamarin da ya janyo cece-ku-ce kan sauya shekarsa zuwa jam’iyyar APC.

Sakataren yada labarai na jam’iyyar NNPP na kasa, Dr Major Agbo, a wani taron manema labarai a Abuja, ya tabbatar wa jam’iyyar cewa babu wani abu a cikin taron, ya kuma bayyana Kwankwaso a matsayin dan siyasar da ba shi da ƙabilanci

“Ba na son ku ji tsoron cewa zai je ko’ina. Ba ya zuwa ko’ina. Kamar yadda na ce, shi mutum ne wanda dangantakarsa ta ko’ina a duk wani dandalin siyasa. Za ku kara ganin hakan,” in ji Agbo.

More News

Mutane uku sun mutu a ruftawar wani ginin bene a Kano

Hukumar Bada Agajin Gaggawa Ta Ƙasa NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane uku bayan da wani bene mai hawa uku ya ruguzo a unguwar...

Ganduje Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Shirya Zanga-Zangar Neman A Sauke Shi

Shugaban jam'iyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin jihar Kano ta jam'iyar NNPP ita ce ke da alhakin shirya zanga-zanga iri...

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miƙata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...