
Gamayyar kungiyoyin ƙwadago sun shirya shiga yajin aiki a ranar 8 ga watan Nuwamba kan yadda akaci zarafin shugaban kungiyar NLC, Kwamared Joe Ajaero.
Haɗakar kungiyar ƙwadago ta NLC da TUC sun gudanar da wani taron manema labarai a ranar Juma’a kan abin da ya faru a jihar Imo.
A ranar Laraba ne aka rawaito wasu jami’an tsaro sun yi awon gaba da Ajaero a hedikwatar kungiyar ta NLC dake Owerri.
Kungiyar NLC ta ce an lakada masa duka lokacin da yake hannun jami’an tsaro zargin da rundunar yan sandan jihar ta musalta inda ta ce wasu batagari ne suka dake shi amma jjami’an yan sandan su ka samu nasarar ceto shi.
A yayin ta taron manema labaran shugabannin ƙwadagon sun yi kira da a binciki kwamishinan yan sandan jihar Imo, Ahmad Barde kana a ɗauke shi daga jihar.
Shugabannin kungiyar sun kuma yi kira da a kama tare da hukunta Nwaneri Chinasa wani mai taimakawa gwamnan jihar da ake zargi jagoranta yan ta’addar da suka kai wa yan kungiyar da kuma ma’aikata farmaki.