Kungiyar boko haram ta kashe ma’aikaciyar agaji

[ad_1]

Hauwa Liman ungozoma ce da ke taimaka wa mata da yara da su ka bar gidajensu kafin a yi garkuwa da ita

Hauwa Liman ungozoma ce da ke taimaka wa mata da yara da su ka bar gidajensu kafin a yi garkuwa da ita

Kungiyar boko haram ta kashe wata ma’aikaciyar kungiyar agaji ta Red Cross wacce mayakan kungiyar su ka yi garkuwa da ita a watan Maris din shekarar nan.

Mayakan kungiyar sun kashe Hauwa Liman, wacce ungozoma ce, ‘yan kawanaki bayan da su ka sa wa’adin.

Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce labarin kashe Hauwa ya daga musu hankali.

Gwamnatin Najeriya ta ce kisan ungozomar rashin imani ne.

  • Buhari ya yi magana da mahaifiyar Leah Sharibu
  • Red Cross: Wa’adin da Boko Haram ta bayar ya kusa cika

An yi garkuwa da Hauwa da wasu sauran ma’aikatan agaji biyu a garin Rann da ke arewacin Njaeriya.

Daya daga cikinsu ita ce Saifura Ahmed Khorsa wacce kungiyar boko haram din ta kashe a watan da ya gabata.

Har yanzu dai, akwai wata daliba ‘yar shekara 15 a hannun mayakan wadanda ke da alaka da kungiyar tada kayar baya ta IS.

Leah Sharibu na daya daga cikin ‘yan makaranta 110 da aka yi garkuwa da su a garin Dapchi da ke arewa maso gabashin Najeriya a watan fabrairun da ya gabata.

More News

Jihar Ogun za ta riƙa biyan ₦77,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun ya amince a riƙa biyan ₦77,000 a matsayin mafi girma ƙarancin albashi a jihar. Sakataren gwamnatin jihar, Tokunbo Tlabi ya...

Kamfanin Maltina ya karrama malamin da ya zama gwarzon shekara

Esomnofu Ifechukwu daga makarantar Crown Grace, Mararaba, jihar Nasarawa, ya zama zakaran gasar Maltina Teacher of the Year karo na 10 a babban taron...

Gwamnatin Enugu ta bayyana dalilin sanya haraji kan gawar mutane

Gwamnatin Jihar Enugu a ranar Lahadi tayi ƙarin haske kan matakin da ta ɗauka kan sanya haraji akan gawar mutane dake ajiye a ɗakin...