Kun san matan da suka fi dukiya a duniya?

MacKenzie Bezos
Hakkin mallakar hoto
Reuters
Image caption

Matar mamallakin kamfanin Amazon

A daidai lokacin da wanda ya fi kowa arziki a duniya da matarsa suka yarda da cewa za su yi rabuwar aure a tsakaninsu, yawan mata a jerin masu kudin duniya na kara yawa.

Hakan ya tabbata a wannan makon, yayin da wanda ya kirkiri kamfanin Amazon Jeff Bezos tare da matarsa MacKenzie suka cimma yarjejeniyar rabuwa da juna.

MacKenzie Bezos za ta ci gaba da rike kashi hudu cikin dari na hannayen jarin kamfanin, wanda darajarsa ta kai dala biliyan 35.6, abin da kuma ya sanya ta zama mace ta uku da ta fi kudi a cikin mata a duniya, sannan kuma ta 24 a duniya idan aka hada da maza.

To su wane ne sauran matan dake kan gaba a duniya, kuma ta yaya suka samu wannan matsayi?

1) Françoise Bettencourt-Meyers

Hakkin mallakar hoto
AFP
Image caption

Matar da tafi ko wacce mace kudi a duniya

Mace ta farko da ta fi kowacce mace kudi a duniya ita ce Françoise Bettencourt-Meyers, wadda yawan kudinta ya kai dala biliyan 49.3, abin da ya sanya ta zama ta 15 da ta fi kowa kudi a duniya, kamar yadda mujallar Forbes ta bayyana.

Wace ce ita?

Matar ‘yar asalin kasar Faransa, ita ta mallaki kusan kashi 33% na hannayen jarin kamfanin kayan kwalliya na L’OrĂ©al cosmetics.

Misis Bettencourt-Meyers mai shekara 65 ta gaji dukiyarta ne daga wajen mahaifiyarta Liliane Bettencourt, wadda ta rasu a watan Satumbar 2017 tana mai shekara 94..

Misis Bettencourt-Meyers kuma malamar jami’a ce ta kuma wallafa littattafai da dama a kan dangantakar Kiristoci da yahudawan Girka.

2) Alice Walton

Hakkin mallakar hoto
Getty Images
Image caption

Mace ta biyu a jerin matan da suka fi kudi a duniya

Alice Walton na da yawan kudin da suka kai dala biliyan 44.4, abin da kuma ya sanya ta zama ta biyu a tsakanin mata kuma ta 17 a duniya idan an hada da maza.

Wace ce ita?

Alice mai shekara 69, ita ce ‘yar Sam Walton, mutumin da ya samar da hamshakin kantin sayar da kayayyaki na Amurka wato Walmart.

To sai dai sabanin ‘yan uwanta biyu Alice ta kaurace wa kamfanin mahaifin nasu, inda ta mayar da hankali wajen kafa kamfanin zane-zane na kashin kanta a garinsu na Bentonville da ke Arkansas.

3) MacKenzie Bezos

Hakkin mallakar hoto
Reuters
Image caption

MacKenzie Bezos

MacKenzie Bezos tana da kudin da yawansu ya kai dala biliyan 35.6- Wannan kudi su ne darajar hannayen jarinta da ke kamfanin na Amazon kadai, amma hakikanin yawan kudinta za su iya fin haka. Sai dai a saurari rahoton mujallar Forbes na 2020 domin ganin yawan kudinta.

Wace ce ita?

Matar mai shekara 48 na da ‘ya’ya hudu tare da mijinta mamallakin kamfanin Amazon, wanda ta aura a shekarar 1993 bayan da suka hadu a lokacin da suke aiki tare a wani kamfani.

Matar ‘yar asalin California na daya daga cikin ma’aikatan farko-farko da kamfanin Amazon ya dauka aiki, inda ta fara a matsayin Akawu. ta kuma wallafa littattafan kagaggun labarai biyu, bayan da ta samu horo daga wani mawallafi mai suna Toni Morrison, wanda kuma ya ce tana daya daga cikin dalibansa da suka fi hazaka.

4) Jacqueline Mars

Hakkin mallakar hoto
Getty Images
Image caption

Mace ta hudu

Adadin yawan kudin Jacqueline Mars ya kai dala biliyan 23.9, abin da kuma ya sanya ta zama ta 33 a duniya.

Wace ce ita?

Matar mai shekara 79 ta mallaki wani bangare na kamfanin Mars, wanda ke daya daga cikin manyan kamfanoni na duniya da ke samar da abincin dabbobi, wanda kakanta Frank ya kafa a shekarar 1911.

Ta yi aiki ga kamfanin danginta na tsawon kusan shekara 20, ta kuma zama cikin manyan daraktocin kamfanin har zuwa shekarar 2026.

A halin yanzu kuma tana daga cikin manyan daraktocin wadansu kamfanoni a Amurka, ana kuma yi mata lakabi da mai taimakon al’ummarta.

5) Yan Huiyan

Tana da yawan kudin da ya kai dala biliyan 22.1, abin da kuma ya sa ta zama mace ta farko da ta fi arziki a China, kuma ta 42 a duniya.

Wzace ce ita?

Matar mai shekara 37 ta mallaki mafiya yawan hannayen jarin hamshakin kamfanin Garden Holdings da ke kasar China, wanda kuma shi ne ya taimaka wajen bunkasa harkokin gine-gine a kasar.

kamar yadda shafin kamfanin ya bayyana shi ne kamfanin gine-gine na uku a fadin duniya a shekarar 2016.

Matshiyar wacce ta kammala karatun digirinta na farko a jami’ar Ohio ta Amurka, ta gaji kusan kashi 57% na hannayen jarin kamfanin daga wajen mahaifinta.

6) Susanne Klatten

Hakkin mallakar hoto
Getty Images
Image caption

Susanne Klatten

Yawan kudinta ya kai dala biliyan 21, abinda ya sanya ta zama ta 46 a duniya.

Wace ce ita?

Matar mai shekara 56 ‘yar asalin Jamus, kuma Baturiya ta biyu a cikin jerin, ta samu arzikin nata ne daga cinikin kananan motoci da kuma magunguna.

Ta gaji kashi 50% na kamfanin sinadarai na Altana AG a lokacin da iyayenta suka rasu, yayin da kuma ita da wani dan uwanta suka mallaki kashi 50% na kamfanin kera kananan motoci na BMW.

Daga bisani kuma ta mallaki kamfin kacokan na Altana AG, tare kuma da sayen hannayen jari a kamfanoni da dama.

7) Laurene Powell Jobs

Hakkin mallakar hoto
Reuters
Image caption

Yawan kudinta ya kai dala biliyan 18.6,

Yawan kudinta ya kai dala biliyan 18.6, kuma ita ce ta 54 a jerin masu kudin duniya.

Wace ce ita?

Tsohuwar matar daya daga cikin wadanda suka kafa kamfanin Apple Steve Jobs, ita da iyalanta sun gaji dala biliyan 20 a hannayen jarin kamfanonin Apple da Disney a lokacinta da mijinta ya rasu.

Tun daga nan ne kuma matar mai shekara 55 ta fara zuba jari a harkar yada labarai, inda ta mallaki mafiya yawan hannyen jarin mujallar Atlantic magazine, tare kuma da zuba jari a wasu mujallun da ba na sayarwa ba.

A watan Mayun 2018 ne dai Misis Powell Jobs ta zuba jarin dala miliyan 16.8 a wasu dakunan kwana shida a wani Otel da ke Francisco.

More News

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miĆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaĆ™i da yiwa tattalin arzikin Ć™asa ne ya hana shi bayyana...