Kun san gwagwarmayar da Zaynab Alkali ta yi?

A zamanin da ba kasafai ake jin muryoyin matan Arewa ba, Zaynab Alkali ta zaburo ta kuma tsunduma cikin harkar rubutun adabi, daga nan kuma tauraruwarta ta fara haskawa.

Littafinta na farko Stillborn ya yi fice a fagen adabi a Najeria, saboda yadda aka kikrkire shi, aka saukaka shi, aka kuma fito da irin gwagwarmayar da matan arewacin kasar ke yi.

Farfesa Zaynab ta zama wata tauraruwa abar koyi ga mata matasa daga arewacin Najeriya saboda rubuce-rubucen da ta ringa yi.

Mun taso muna karanta litattafanta, don haka babban alfahari ne a gare ni a ce na samu tattauna wa da ita.

Na gano cewa mace ce mai jajirce wa da ta yi fice har ake dangata ta da gwagwarmayar kwato ‘yancin mata a shekarun 1980.

Na gano cewa uwa ce da ta sadaukar da rayuwarta ga ‘ya’yanta, sannan mata ce da ta damu da ci gaban alummarta.

Da fatan za ku ji dadin yadda tattaunawar ta mu ta kasance.

More News

Mutane uku sun mutu a ruftawar wani ginin bene a Kano

Hukumar Bada Agajin Gaggawa Ta Ƙasa NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane uku bayan da wani bene mai hawa uku ya ruguzo a unguwar...

Ganduje Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Shirya Zanga-Zangar Neman A Sauke Shi

Shugaban jam'iyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin jihar Kano ta jam'iyar NNPP ita ce ke da alhakin shirya zanga-zanga iri...

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...