
Wata kotun shari’ar Muslunci dake Kano ta aike da Murja Ibrahim Kunya ya zuwa gidan yari.
Kotun ta kuma dage shari’ar da ake mata ya zuwa ranar 16 ga watan da muke ciki.
Ana dai tuhumar Murja da yin kalaman da suka haɗa zagi da kuma kalaman batsa a shafin ta na Tik Tok dake da mabiya masu yawan gaske.