Kotu ta hana VIO kamawa, tsare motoci ko cin tarar direbobi a kan hanya

Justis Evelyn Maha ta Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta bayar da umarni da ya hana Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa, wanda aka fi sani da VIO daga tsayarwa, kwace, ko kama motocin da ke kan hanya.

Kotun ta kuma hana Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawan daga kakabawa direbobi tara.

Hukuncin da aka yanke a ranar 2 ga Oktoba ta hannun Justis Maha ya samo asali ne daga karar kare hakkin dan Adam da wani mai fafutukar kare hakkin dan Adam kuma lauya mai kare muradun jama’a, Abubakar Marshal, ya shigar.

A cikin hukuncin, Justis Maha ta amince da hujjojin da mai shigar da kara ya gabatar cewa babu wata doka da ta ba da izini ga VIO da jami’anta su tsayar, kwace, ko kama motoci ko kuma su kakaba wa direbobi tara.

Related Articles