
Kotun daukaka dake Abuja ta dakatar da hukumar zabe mai zaman manta ta INEC gudanar da sabon zabe na kujerun yan majalisar dokokin jihar Rivers da suka sauya sheka.
Alkalin kotun, Donatus Okorowo shi ne ya bayar da umarnin a ranar Juma’a.
A ranar 11 ga watan Disamba mambobin majalisar dokokin jihar Rivers 27 suka sauya sheka daga jam’iyar PDP ya zuwa jam’iyar adawa ta APC.
Hakan ya sa kakakin majalisar dokokin jihar, Edison Ehie ya ayyana cewa kujerun yan majalisar babu kowa akansu kuma Ya yi kira ga hukumar zabe ta INEC da ta gudanar da sabon zabe a mazabunsu.
Biyo bayan umarnin shugaban majalisar ne yasa masu sauya shekar garyawa gaban kotu.