Kotu ta ci gaba da tsare wacce ta kashe Nafiu

Wata kotun majistare da ke Kano, a ranar Laraba, ta bayar da umarnin a tsare wata matar aure ‘yar shekara 24, Hafsat Surajo, a gidan gyaran hali bisa zarginta da daba wa mai taimako a gidanta, Nafiu Hafizu, ɗan shekara 38, wuka har lahira.

Wacce ake tuhumar kuma wacce ke zaune a Unguwa Uku Quarters Kano, ta gurfana ne a gaban kuliya bisa tuhume-tuhume biyu na yunkurin kashe kanta da kuma kisan kai.

Alkaliyar kotun Majistare Hadiza Abdulrahman ta bayar da umarnin a tsare wacce ake kara a gidan gyaran hali da ke jihar.

Ta dage ci gaba da shari’ar har zuwa ranar 1 ga Fabrairu, 2024 don ci gaba da sauraro.

More from this stream

Recomended