Kotun zaben jihar Filato ta kori Bali Napoleon na PDP a matsayin Sanatan Filato ta Kudu.
Ta kuma bayyana Simon Lalong na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar sanatan.
Idan ba a manta ba, Lalong kwanan nan aka naɗa shi a matsayin Ministan Kwadago da Aiki, da shugaba Tinubu ya yi.