Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya ce bai taɓa samun matsala da Gareth Bale ba

Gareth Bale

Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya ce “ban taɓa samun matsala da Gareth Bale ba”, a yayin da dan wasan na Wales yake shirin tafiya domin zaman aro a Tottenham.

Raunukan da ya rika ji, da rashin tagomashinsa da kuma rahotannin rashin jituwa tsakaninsa da Zidane ya sa an mayar da shi saniyar-ware a Madrid.

Zidane yace bai yi magana da Bale kafin ya tafi London.

Har yanzu Tottenham ba ta bayyana daukar Bale ba kuma a yau Asabar Zidane ya ce “ba mu cimma matsaya ba”.

“Lamarin na da rikitarwa. Shi Bale a kodayaushe ya fi son ya samu abin da yake so. Amma ni ban taba samun matsala da Gareth ba”, in ji Zidane.

“Akwai abubuwan da ke faruwa a kodayaushe. Yana so ya samu sauyi yanzu don haka babu abin da za mu ce sai fatan alheri a gare shi. Irin wadannan abubuwa suna faruwa a kwallon kafa amma ni kodayaushe ina cewa shi dan wasa ne na musamman.”

Bale ya lashe Kofin Zakarun Turai hudu, Kofin La Liga biyu, Kofin Copa del Rey daya, Kofin Uefa Super Cups uku da kuma Kofin Duniya na kungiyoyi uku a Real kuma ya ci kwallo fiye da 100.

Shi ne dan wasan Ingila mafi tsada a tarihi, kuma si ne dan kasar Ingila da ya fi zura kwallo a gasar La Liga – inda ya ci kwallo 80 sannan ya taimaka aka ci 40 a wasanni 171 da ya buga na lig.

More News

Kotu Ta Hana PDP Cire Shugaban Riƙon Jam’iyar

Wata Babbar Kotun Tarayya dake Abuja ta hana jam'iyar PDP dakatar da Umar Damagum daga matsayinsa na shugaban riƙon jam'iyar. Mai Shari'a  Peter Lifu shi...

Tinubu Ya Dawo Abuja Daga Ziyarar Aiki Da Ya Kai  Saudiya da Nezaland

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya dawo Abuja bayan ziyarar aiki da ya kai ƙasashen Saudiya da Nezaland. A ranar 22 ga watan Afrilu ne...

CBN ya dakatar da kudirinsa na sa bankuna su riƙa cajar kwastomominsu

Babban bankin Najeriya ya umarci bankunan da su dakatar da cajin kudaden ajiya har zuwa ranar 30 ga Satumba, 2024.Babban bankin ya bayyana hakan...

Ƴansanda sun kama likitan bogi

Rundunar ‘yan sanda ta Zone 2, Onikan, Legas, ta kama wani likitan jabu mai shekaru 37, kuma ma’aikacin lafiya, tare da zargin amfani da...